Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Zion: Restoration of, promised

21 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da Restoration of, promised

  1. Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa.

  2. Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.

  3. Na sa maganata a bakinka na kuma rufe ka da inuwar hannuna, Na shimfiɗa sammai, na kafa harsashen duniya, na kuma ce wa Sihiyona, ‘Ku mutanena ne.’ ”

  4. Ki farka, ki farka, ya Sihiyona, ki sanya wa kanki ƙarfi. Ki sa rigarki na daraja, Ya Urushalima, birni mai tsarki. Marasa kaciya da maƙazanta ba za su shi cikinki ba.

  5. Ki kakkaɓe ƙurarki; ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima. Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki, Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.

  6. Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”

  7. Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu; tare sun yi sowa ta farin ciki. Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona, za su gan shi da idanunsu.

  8. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.

  9. ’Ya’ya maza masu zaluntarku za su zo suna rusunawa a gabanki; dukan waɗanda suka rena ki za su rusuna a ƙafafunki su kuma ce da ke Birnin Ubangiji, Sihiyona na Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

  10. Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto; Dutsen zai zama mai tsarki, gidan Yaƙub kuma zai mallaki gādonsa.

  11. Masu kawo ceto za su haura zuwa Dutsen Sihiyona don su yi mulkin duwatsun Isuwa. Ubangiji ne zai yi mulki.

  12. Ki rera, ya Diyar Sihiyona; ki tā da murya, ya Isra’ila! Ki yi murna ki kuma yi farin ciki da dukan zuciyarki, Ya Diyar Urushalima!

  13. A wannan rana za su cewa Urushalima, “Kada ki ji tsoro, ya Sihiyona; kada ki bar hannuwanki su raunana.

  14. Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona,

  15. “Ci gaba da yin shela, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Garuruwana za su sāke kwarara da wadata, Ubangiji kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta’aziyya, yă kuma zaɓi Urushalima.’ ”

  16. “Zo, ya ke Sihiyona! Ku tsere, ku masu zama a cikin Diyar Babilon!”

  17. “Ki yi sowa ki yi murna, ya ke Diyar Sihiyona. Gama ina zuwa, zan zauna a cikinki,” in ji Ubangiji.

  18. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ina kishin Sihiyona ƙwarai; ina kuma cike da kishi dominta.”

  19. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.”

  20. Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.

  21. Zan lanƙwasa Yahuda yadda nake lanƙwasa bakana, in kuma cika ta da Efraim kamar kibiya. Zan tā da ’ya’yanki maza, ya Sihiyona, gāba da ’ya’yanki, ya Girka, in kuma mai da ke kamar takobin jarumin yaƙi.