Jebus
An kuma san shi da: Jebusi
31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps
Ayoyin da suka ambaci Jebus
Zela, Hayelef, birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima), Gibeya da Kiriyat, garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu. Wannan shi ne rabon gādon kabilar Benyamin bisa ga iyalansu.
Amma bai so ya sāke kwana a can ba, mutumin ya tashi ya tafi ya bi ta Yebus (wato, Urushalima), tare da jakunansa biyu da aka yi musu shimfiɗa da kuma ƙwarƙwaransa.
Sa’ad da suka yi kusa da Yebus dare kuma ya riga ya yi, bawan ya ce wa maigidansa, “Mu dakata a birnin nan na Yebusiyawa mu kwana.”
Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin
suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.