Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Young Men

347 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.

  2. Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

  3. Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

  4. Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani?

  5. Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.

  6. Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.

  7. Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce.

  8. Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,

  9. in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,

  10. to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka!

  11. Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma.

  12. Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.

  13. Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

  14. Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,

  15. duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

  16. Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?

  17. Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,

  18. talauci kuwa zai zo kamar ’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.

  19. Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,

  20. wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,

  21. wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye

  22. Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.

  23. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

  24. duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,

  25. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,