Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Young Men

347 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.

  2. Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.

  3. Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.

  4. Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.

  5. La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali.

  6. Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.

  7. Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.

  8. Ku saurara ’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi.

  9. Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.

  10. Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,

  11. ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.

  12. Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.

  13. Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.

  14. Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.

  15. Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.

  16. Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”

  17. Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.

  18. Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.

  19. Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba.

  20. Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne.

  21. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.

  22. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.

  23. Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani.

  24. Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su.

  25. Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.