Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Trumpet: Used at the anointing of kings

4 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Used at the anointing of kings

  1. A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’

  2. Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!”

  3. Sai suka yi sauri suka ɗauki rigunansu suka shimfiɗa a ƙasa, suka busa kakaki, suka yi ihu, suka ce, “Yehu ne sarki.”

  4. Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”