Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Trumpet: Blowing at all religious processions and ceremonies

5 ayoyi · 46 fannoni

Ayoyi game da Blowing at all religious processions and ceremonies

  1. Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni.

  2. Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.

  3. Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.

  4. Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije,

  5. Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni.