Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Treaty

40 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa.

  2. Ina niyya in gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, yadda Ubangiji ya faɗa wa mahaifina Dawuda, sa’ad da ya ce, ‘Ɗanka wanda zai gāje ka, shi zai gina haikali domin Sunana.’

  3. “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”

  4. Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”

  5. Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir.

  6. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”

  7. A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata.

  8. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.

  9. Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya.

  10. A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki,

  11. sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki.

  12. Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba.

  13. Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul, sunan da suke da shi har wa yau.

  14. Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 120 na zinariya.

  15. Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi.