Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Treaty

40 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko.

  2. “Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu.

  3. Kafin ’yan leƙen asirin su kwanta, sai ta tafi wurinsu a bisa rufin ɗakin

  4. ta ce musu, “Na sani Ubangiji ya riga ya ba ku ƙasan nan, tsoronku kuma ya kama mu har zukatan mazaunan ƙasar duka sun narke saboda ku.

  5. Mun ji yadda Ubangiji ya busar da ruwan Jan Teku domin ku lokacin da kuka fito daga ƙasar Masar, da kuma abin da kuka yi wa Sihon da Og, sarakunan nan biyu na Amoriyawa gabas da Urdun, waɗanda kuka hallaka su sarai.

  6. Da muka ji labarin, duk sai zuciyar kowa ta narke, kowa ya karaya saboda ku, gama Ubangiji Allahnku shi ne Allah na sama da ƙasa.

  7. Yanzu ina roƙonku ku rantse mini da Ubangiji cewa za ku yi wa iyalina alheri kamar yadda na yi muku alheri. Ku ba ni ƙwaƙƙwarar shaida cewa

  8. za ku ceci rayukan mahaifina da mahaifiyata, da ’yan’uwana maza da mata, da duk waɗanda suke nasu, za ku cece mu daga mutuwa.”

  9. Mutanen suka tabbatar mata suka ce, “Ranmu a bakin ranki! In ba ki faɗa wa kowa abin da ya kawo mu ba, za mu yi miki alheri da aminci lokacin da Ubangiji ya ba mu ƙasar.”

  10. Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.

  11. Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”

  12. Mutanen suka ce mata, “Rantsuwar da kika sa muka yi, ba za tă yi amfani ba

  13. sai in kin ɗaura jan ƙyalle a tagar da kika zura mu, kuma sai in kin kawo mahaifinki da mahaifiyarki, da ’yan’uwanki, da dukan iyalinki cikin gidanki.

  14. In wani ya fita kan hanya, alhakin jininsa yă kasance a kansa; ba ruwanmu. Amma in aka taɓa wani da yake cikin gidanki tare da ke, alhakin jininsa yana kanmu.

  15. In kika tone mana asiri, za mu karya alkawarin da kika sa muka yi.”

  16. Ta ce, “Na yarda! Bari yă zama yadda kuka ce.” Sai ta sallame su suka tafi. Ta kuwa ɗaura jan ƙyalle a tagar.

  17. Kwana uku bayan sun yi alkawari da Gibeyonawa, sai Isra’ilawa suka ji cewa Gibeyonawa maƙwabtansu ne, waɗanda suke zaune kurkusa da su.

  18. Saboda haka Isra’ilawa suka tashi a rana ta uku suke je biranen mutanen, wato, Gibeyon, Kefira, Beyerot da Kiriyat Yeyarim.

  19. Amma Isra’ilawa ba su kai musu hari ba domin shugabanninsu sun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane Isra’ila duka kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.

  20. Amma shugabanni suka amsa musu suka ce, “Mun rantse musu da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, saboda haka ba za mu taɓa su ba yanzu.

  21. Ga abin da za mu yi musu, za mu bar su da rai don kada fushin Allah yă sauka a kanmu gama mun riga mun rantse musu.”

  22. Suka ƙara da cewa, “Mu bar su da rai, amma bari su zama masu yankan itace da masu ɗibo mana ruwa.” Haka shugabannin suka cika alkawarinsu.

  23. Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa.

  24. Solomon ya mayar da wannan saƙo ga Hiram ya ce,

  25. “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.