Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Timothy

38 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bulus ya kai Derbe sa’an nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa mutuniyar Yahuda ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.

  2. ’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa.

  3. Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.

  4. Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya.

  5. Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.

  6. Sa’ad da Sila da Timoti suka iso daga Makidoniya, sai Bulus ya ba da kansa ga yin wa’azi kaɗai, yana tabbatar wa Yahudawa cewa Yesu shi ne Kiristi.

  7. Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.

  8. Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya.

  9. Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris,

  10. inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya.

  11. Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi.

  12. Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina.

  13. Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

  14. In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.

  15. Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da ’yan’uwa.

  16. Gama Ɗan Allah, Yesu Kiristi, wanda ni da Sila da Timoti muka yi muku wa’azinsa, ai, ba “I” da “A’a” ba ne, amma a cikin Kiristi, “I” ne kullum.

  17. Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku.

  18. Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku.

  19. Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.

  20. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.

  21. Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan.

  22. Muka aiki Timoti, wanda yake ɗan’uwanmu da kuma abokin aikin Allah a cikin yaɗa bisharar Kiristi, don yă gina ku yă kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku,

  23. Amma ga shi yanzu Timoti ya dawo mana daga wurinku ya kuma kawo labari mai daɗi game da bangaskiyarku da kuma ƙaunarku. Ya faɗa mana yadda kullum kuke da tunani mai kyau a kanmu, yadda kuke marmari ku gan mu, kamar dai yadda mu ma muke marmari mu gan ku.

  24. Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu da kuma na Yesu Kiristi begenmu,

  25. Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.