Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Timothy: Paul's love for

7 ayoyi · 18 fannoni

Ayoyi game da Paul's love for

  1. Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

  2. Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.

  3. Zuwa ga Timoti ɗana na gaske cikin bangaskiya. Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

  4. Timoti, ɗana, na ba ka wannan umarni bisa ga annabce-annabcen da aka yi a dā game da kai, domin ta wurin binsu ka iya yin yaƙi mai kyau,

  5. Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana. Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

  6. Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina.

  7. Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki.