Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Reward of Saints: Sitting in judgment with Christ

4 ayoyi · 51 fannoni

Ayoyi game da Sitting in judgment with Christ

  1. sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki.

  2. Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.

  3. Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.

  4. Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan.