Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Power of the Holy Spirit

30 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

  2. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.

  3. Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.

  4. Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya.

  5. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, waɗannan ƙasusuwa su ne dukan gidan Isra’ila. Suna cewa, ‘Ƙasusuwanmu sun bushe, sa zuciyarmu duk ya tafi; an share mu ƙaf.’

  6. Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila.

  7. Sa’an nan ku, mutanena, za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na buɗe kaburburanku na fitar da ku daga cikinsu.

  8. Zan sa Ruhuna a cikinku za ku kuwa rayu, zan kuma zaunar da ku a ƙasarku. Sa’an nan za ku san cewa Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata, in ji Ubangiji.’ ”

  9. Amma game da ni, ina cike da iko ta wurin Ruhun Ubangiji da kuma adalci da ƙarfi, don a sanar da Yaƙub laifofinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa.

  10. Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  11. “Kai mene ne, ya babban dutse? A gaban Zerubbabel za a rushe ka ka zama fili. Sa’an nan Zerubbabel yă kawo dutsen da ya fi kyau, a kuma yi ta sowa ana cewa, ‘Allah yă yi masa albarka! Allah yă yi masa albarka!’ ”

  12. Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

  13. Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

  14. Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka.

  15. Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

  16. Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”

  17. Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”

  18. Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.

  19. amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.

  20. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.

  21. Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa.

  22. Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

  23. ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi.

  24. Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu,

  25. Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.