Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strangers in Israel: Admitted to worship in the outer court of the temple

5 ayoyi · 33 fannoni

Ayoyi game da Admitted to worship in the outer court of the temple

  1. “Game da baƙo kuwa wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba, amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka,

  2. gama mutane za su ji game da girman sunanka, da ƙarfin hannunka, da kuma hannunka mai iko, sa’ad da ya zo, ya yi addu’a yana fuskantar wannan haikali,

  3. ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi dukan abin da baƙon ya tambaye ka, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, bari kuma su san cewa wannan gidan da na gina, ya amsa Sunanka.

  4. Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu.

  5. Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42.