Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Strangers in Israel: To have the gleaning of the harvest

6 ayoyi · 33 fannoni

Ayoyi game da To have the gleaning of the harvest

  1. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  2. “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

  3. Sa’ad da kuke girbi a gonarku, sai kuka manta da dami, kada ku koma don ku ɗauka. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa, saboda Ubangiji Allahnku yă albarkace ku a cikin dukan aikin hannuwanku.

  4. Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.

  5. Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.

  6. Ku tuna dā ku bayi ne Masar. Shi ya sa na umarce ku ku yi wannan.