Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Spiritual Peace

65 ayoyi · 53 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi; zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi,

  2. ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila. Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,” in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.”

  3. “Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna.

  4. Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Zan fadada salama gare ta kamar kogi, wadatar al’ummai kuma kamar rafi mai gudu; za ku tsotsa a kuma riƙe ku a hannunta ku kuma yi wasa a gwiwoyinta.

  5. Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya.

  6. “ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.

  7. “ ‘Zan yi alkawarin salama da su in kuma kawar wa ƙasar da namun jeji domin su zauna a hamada su kuma kwana a kurmi lafiya lau.

  8. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.”

  9. Zan ƙwace kekunan yaƙi daga Efraim, da kuma dawakan yaƙi daga Urushalima, za a kuma karya bakan yaƙi. Zai yi shelar salama ga al’ummai. Mulkinsa zai yaɗu daga teku zuwa teku, daga Kogi kuma zuwa ƙarshen duniya.

  10. “Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai.

  11. don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”

  12. “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”

  13. “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.

  14. “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’

  15. kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki.

  16. Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.

  17. “Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”

  18. Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.

  19. ba su kuma san hanyar salama ba.”

  20. Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,

  21. Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama;

  22. Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”

  23. Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,

  24. Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

  25. Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.