Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Soldiers

65 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Bulus ya kai bakin matakala, sai da sojoji suka ɗaga shi sama saboda tsananin haukan taron.

  2. sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka.

  3. Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”

  4. Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”

  5. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Bulus ya ce, “I.”

  6. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.”

  7. Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai saba’in da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.

  8. Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris.

  9. Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja.

  10. Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus.

  11. Sa’ad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ’yan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki.

  12. Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.”

  13. Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere.

  14. Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci.

  15. Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa.