Skip to content

Simon

3 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Simon

  1. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.

  2. Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.

  3. Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.