Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Soldiers

65 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Hafsoshi za su ce wa mayaƙa, “Ko akwai wanda ya gina sabon gida bai kuma buɗe shi ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă buɗe shi.

  2. Ko akwai wani da ya shuka inabi, bai kuwa fara jin daɗinsa ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă ji daɗinsa.

  3. Ko akwai wani da aka yi masa alkawarin mata, bai kuwa aure ta ko ba? Bari yă tafi gida, kada yă mutu a yaƙi, wani dabam yă aure ta.”

  4. Sa’an nan hafsoshin za su ƙara da cewa, “Ko akwai wani da yake tsoro, ko ya karai? Bari yă tafi gida don kada ’yan’uwansa su karai su ma.”

  5. Sa’ad da hafsoshin suka gama magana da mayaƙan, sai su naɗa komandodi a kansu.

  6. In mutum bai daɗe da aure ba, kada a sa yă je yaƙi, ko yă yi wani aiki. Gama zai huta shekara guda a gida, yă faranta wa matar da ya aura rai.

  7. ka yi shela ga mutane yanzu cewa, ‘Duk wanda ya yi rawan jiki don tsoro, sai yă juya yă bar Dutsen Gileyad.’ ” Saboda haka mutum dubu ashirin da biyu suka koma, sai mutum dubu goma suka rage.

  8. Za mu ɗauko mutum goma a kowane mutum ɗari daga dukan kabilan Isra’ila, da ɗari a dubu, da kuma dubu a dubu goma, domin a tanada wa mayaƙan. Sa’an nan, sa’ad da mayaƙan suka iso Geba a Benyamin, za su yi da su daidai bisa ga muguntar da suka yi a Isra’ila.”

  9. Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.

  10. Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.

  11. Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga.

  12. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”

  13. Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.

  14. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

  15. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.

  16. Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).

  17. A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.

  18. Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.

  19. Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.

  20. Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

  21. Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.”

  22. Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru.

  23. Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa.

  24. Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’

  25. In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.”