Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Soldiers: Crucified Jesus

19 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Crucified Jesus

  1. Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.

  2. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

  3. Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.

  4. Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).

  5. A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.

  6. Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.

  7. Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.

  8. Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

  9. Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.

  10. Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.

  11. Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”

  12. Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a.

  13. Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.

  14. Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.

  15. Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).

  16. Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.

  17. Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.

  18. Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.

  19. Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce, “Suka rarraba tufafina a junansu, suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan.