Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Silver: Sockets for the boards of the tabernacle

7 ayoyi · 57 fannoni

Ayoyi game da Sockets for the boards of the tabernacle

  1. ka kuma yi rammuka arba’in da azurfar da za a sa wa katakan nan ashirin. Za a sa kawunan katakan da aka fiƙe a cikin rammukan.

  2. Ta haka za a sami katakai takwas da rammukansu na azurfa guda goma sha shida, kowane katako yana da rammuka biyu.

  3. Ka rataye shi a bisa dogayen sanduna huɗun nan na itacen ƙirya, waɗanda aka dalaye da zinariya, waɗanda suke tsaya a rammuka huɗu na azurfa.

  4. suka kuma yi rammukan azurfa arba’in don katakan su shiga ƙarƙashinsu, rammuka biyu domin kowane katako, ɗaya ƙarƙashin kowanne da aka fiƙe.

  5. da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako.

  6. Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako.

  7. Suka yi dogayen sanduna huɗu na itacen ƙirya dominsa, suka dalaye su da zinariya. Suka yi ƙugiya na zinariya dominsa, suka yi rammuka huɗu da azurfa.