Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Seekers

165 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!

  2. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”

  3. Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Na Asaf. Zabura ce. Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni.

  5. Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.

  6. Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana. Sela

  7. ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana.

  8. Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa;

  9. na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.

  10. “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?

  11. Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?

  12. Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?” Sela

  13. A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.

  14. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.

  15. Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.

  16. Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.

  17. Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.

  18. Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.

  19. Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.

  20. Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.

  21. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.

  22. Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela

  23. Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.

  24. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.

  25. in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,