Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Salutations

69 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.

  2. Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.

  3. ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.

  4. Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba tă daina sumbar ƙafafuna ba.

  5. Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa,

  6. “Sa’ad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’

  7. Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”

  8. Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

  9. Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina.

  10. Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.

  11. Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan ’yan Ikkilisiya, yana gaishe ku. Erastus, mai bi da ayyukan jama’ar gari, da kuma ɗan’uwanmu Kwartus, suna gaishe ku.

  12. Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.

  13. Dukan tsarkaka suna gaishe ku.

  14. Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu. ’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.

  15. Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yă kasance tare da ku.

  16. Ni, Bulus, nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna, wannan ce shaida a kowace wasiƙata, haka nake rubutu.

  17. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi.

  18. ’Ya’yan ’yar’uwarki wadda Allah ya keɓe, suna gaishe ku.

  19. Ina fata in gan ka nan ba da daɗewa ba, za mu kuwa yi magana fuska da fuska.