Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sackcloth

36 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.

  2. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.

  3. Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba.

  4. Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.”

  5. Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”

  6. Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai.

  7. Sai suka ce, “Mutumin ya sa riga mai gashi, ya kuma yi ɗamara da fata.” Sarkin ya ce, “Ai, Iliya mutumin Tishbe nan ne.”

  8. Da sarki ya ji maganar macen sai ya yage rigunansa. Sa’ad da sarki yake wucewa a kan katangar birnin, sai mutane suka gan yana saye da rigar makoki a ciki.

  9. Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji.

  10. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz.

  11. A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu.

  12. Sa’ad da Mordekai ya sami labari game da dukan abin da aka yi, sai ya yayyage rigunansa, ya sanya tsummokin makoki, ya zuba toka a kā, ya kuma shiga ciki birni yana kuka mai zafi da ƙarfi.

  13. Amma ya kai bakin ƙofar sarki ne kawai, gama ba a yarda wani sanye da tsummokin makoki yă shiga cikin birni ba.

  14. “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

  15. Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

  16. sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.

  17. A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana.

  18. A tituna sun sa tsummoki a jikunansu; a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa dukansu sai makoki suke yi, sun kwanta suna kuka.

  19. a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

  20. Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki ya kira ku a wannan rana don ku yi kuka ku yi ihu, don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.

  21. Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

  22. Na suturar da sararin sama da duhu na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”

  23. Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba.

  24. Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki ku yi birgima a toka; ku yi kuka mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, gama nan da nan mai hallakarwa zai auko mana.

  25. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.