Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sackcloth: A symbol of mourning

11 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da A symbol of mourning

  1. Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.”

  2. Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”

  3. “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.

  4. A tituna sun sa tsummoki a jikunansu; a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa dukansu sai makoki suke yi, sun kwanta suna kuka.

  5. Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba.

  6. Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki ku yi birgima a toka; ku yi kuka mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, gama nan da nan mai hallakarwa zai auko mana.

  7. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.

  8. Dattawan Diyar Sihiyona sun zauna shiru a ƙasa; suka kuma sa rigar buhu. ’Yan matan Urushalima suka sunkuyar da kawunansu ƙasa.

  9. Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba. Fuskokinsu kuma za su rufu da kunya a kuma aske kawunansu.

  10. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.

  11. Ku yi makoki kamar budurwa a cikin tsummoki tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.