Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Religious Zeal

726 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama.

  2. Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”

  3. Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya.

  4. Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu.

  5. Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe.

  6. Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,

  7. suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”

  8. Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.

  9. Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya,

  10. kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.

  11. Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu.

  12. Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai.

  13. Suka kuma jima a can tare da almajirai.

  14. mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.

  15. Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.

  16. Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.

  17. Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ’yan’uwa.

  18. Bayan suka yi ’yan kwanaki a can, sai ’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su.

  19. Notwithstanding it pleased Silas to abide there still.

  20. Amma Bulus da Barnabas kuwa suka dakata a Antiyok, inda su da waɗansu da yawa suka yi koyarwa suka kuma yi wa’azin maganar Ubangiji.

  21. Bayan ’yan kwanaki sai Bulus ya ce wa Barnabas, “Mu koma mu ziyarci ’yan’uwa a duk garuruwan da muka yi wa’azin bisharar Ubangiji mu ga yadda suke.”

  22. Ya ratsa ta Suriya da Silisiya, yana ƙarfafa ikkilisiyoyi.

  23. Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.

  24. A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana.

  25. Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.”