Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reasoning: The gospel cannot be explained by

25 ayoyi · 8 fannoni

Ayoyi game da The gospel cannot be explained by

  1. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.

  2. Gama a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”

  3. Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba?

  4. Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.

  5. Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima,

  6. amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai,

  7. amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah.

  8. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

  9. ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa.

  10. Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya.

  11. Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja,

  12. Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba.

  13. Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.

  14. Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai.

  15. Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu,

  16. domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

  17. Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba.

  18. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai.

  19. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba.

  20. Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

  21. Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.

  22. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.

  23. Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake.

  24. Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.

  25. Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.