Skip to content

Felix

8 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Felix

  1. Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.”

  2. Kalaudiyus Lisiyas. Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis. Gaisuwa.

  3. Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.

  4. Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.”

  5. Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.

  6. Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.”

  7. Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.

  8. Da yake za su yi kwanaki da dama a can, sai Festus ya tattauna batun Bulus da sarki. Ya ce, “Akwai mutumin da Felis ya bari a daure.