Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prudence

192 ayoyi · 40 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.

  2. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”

  3. To, mutanen Efraim suka ce wa Gideyon, “Me ya sa ka yi mana haka? Me ya sa ba ka kira mu lokacin da ka tafi yaƙi da Midiyawa ba?” Suka zarge shi sosai.

  4. Amma ya ce musu, “Me na yi da za a iya kwatanta da abin da kuka yi? Ashe, kalar inabin da Efraim ta yi bai fi dukan girbin inabin da Abiyezer suka yi ba?

  5. Allah ya ba da Oreb da Zeyib, shugabannin Midiyawa a hannuwanku. Me na yi da ya fi naku? Da ya faɗi haka sai hankalinsu ya kwanta.”

  6. Ɗaya daga cikin bayin ya ce, “Na san wani yaro, ɗan Yesse na Betlehem, ya iya kiɗan molo, yana da hikima, shi kuma ya iya yaƙi. Ya iya magana, ga shi kuma kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”

  7. Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa.

  8. Ta fāɗi a ƙafafunsa ta ce, “Bari laifin yă zama nawa, ranka yă daɗe. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka ji abin da baiwarka za tă ce.

  9. Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba.

  10. Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal.

  11. Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka.

  12. Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye.

  13. Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa.

  14. Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila,

  15. kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.”

  16. Da Dawuda ya isa ƙwanƙoli, inda mutane sun saba yi wa Allah sujada, Hushai, mutumin Arkitawa kuwa yana can don yă tarye shi, taguwarsa a yage, ga kuma ƙura a kansa.

  17. Sai Dawuda ya ce masa, “In ka tafi tare da ni, za ka zama mini kaya.

  18. Amma in ka koma birni, ka gaya wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; dā ni bawan mahaifinka ne, amma yanzu zan zama bawanka,’ ta haka za ka watsar da shawarar Ahitofel.

  19. Da Hushai ya zo wurinsa, sai Absalom ya ce, “Ahitofel ya ba da wannan shawara. Mu yi abin da ya ce? In ba haka ba, sai ka ba mu ra’ayinka.”

  20. Hushai ya ce wa Absalom, “Shawarar da Ahitofel ya bayar a wannan lokaci kam, ba ta da kyau.

  21. Ka san mahaifinka da mutanensa mayaƙa ne, suna cikin fushi kamar mugun beyar da aka ƙwace mata ’ya’ya. Ban da haka ma, mahaifinka gogagge ne a yaƙi; ba zai kwana da rundunar ba.

  22. Kai, ko yanzu ma, ya riga ya ɓuya cikin kogo ko kuma a wani wuri. In har ya fara kai wa rundunarka hari duk wanda ya ji, zai ce, ‘An yi kaca-kaca da rundunar da suka bi Absalom.’

  23. Kai, ko jarumi mai zuciya kamar na zaki ma, zai narke don tsoro, gama dukan Isra’ila sun sani mahaifinka mayaƙi ne, sun kuma san cewa waɗanda suke tare da shi jarumawa ne.

  24. “Saboda haka ina ba ka shawara, bari a tara maka dukan Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba da yawansu ya yi kamar yashin bakin teku, kai kanka ka jagorance su zuwa fagen fama.

  25. Sa’an nan za mu fāɗa masa duk inda yake, za mu fāɗa masa kamar yadda raɓa takan fāɗo a bisa ƙasa. Da shi da mutanensa babu ko ɗaya da za a bari da rai.