Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prudence: Necessity for-Illustrated.

7 ayoyi · 40 fannoni

Ayoyi game da Necessity for-Illustrated.

  1. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.

  2. “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

  3. “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.

  4. Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a,

  5. yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’

  6. “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya ƙarawa da mai zuwa da dubu ashirin?

  7. In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama.