Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Private Prayer

60 ayoyi · 28 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba.

  2. Sa’an nan a lokacin miƙa hadaya na yamma, na tashi da ɓacin raina, da yagaggun kayana, na durƙusa na miƙa hannuwana sama ga Ubangiji Allahna

  3. na kuma yi addu’a, na ce, “Ya Allah, ina cike da kunya, ba zan iya ɗaga fuskata gare ka ba, ya Allahna, domin zunubanmu sun fi mu tsayi, tudunsu har ya kai sama.

  4. Sai sarki ya ce mini, “Me kake so?” Sai na yi addu’a ga Allah na sama,

  5. Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.

  6. Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.

  7. Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannotmaskil na Heman dangin Ezra. Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.

  8. “Bayan na ba da takardun ciniki ga Baruk ɗan Neriya, sai na yi addu’a ga Ubangiji na ce,

  9. “A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.

  10. Kakan nuna ƙauna ga dubbai amma kakan hukunta ’ya’ya saboda laifin ubanninsu a bayansu. Ya mai girma da kuma Allah mai iko, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki,

  11. manufofinka da girma suke, ayyukanka kuma masu girma ne. Idanunka suna a buɗe ga dukan hanyoyin mutane; kakan sāka wa kowa gwargwadon halinsa yadda ya dace.

  12. Ka aikata ayyukan banmamaki da kuma al’ajabai a Masar ka kuma ci gaba da su har yă zuwa yau, a Isra’ila da kuma a cikin dukan ’yan adam, ka kuma sami sunan da har yanzu yake naka.

  13. Ka fitar da mutanenka Isra’ila daga Masar da alamu da abubuwa banmamaki, ta wurin hannu mai iko da kuma hannu mai ƙarfi tare da banrazana mai girma.

  14. Ka ba su wannan ƙasa da ka rantse za ka ba wa kakanni kakanninsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.

  15. Suka shiga suka mallake ta, amma ba su yi maka biyayya ba, ba su kuma bi dokarka ba; ba su yi abin da ka umarce su ba. Saboda haka ka kawo masifa a kansu.

  16. “Duba yadda aka gina mahaurai don a kame birni. Saboda takobi, yunwa da annoba, za a ba da birnin ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye shi da yaƙi. Abin da ka faɗa ya faru, yadda kake gani yanzu.

  17. Ko da yake za a ba da birnin ga Babiloniyawa, kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka ce mini, ‘Saye fili da azurfa ka kuma sa a shaida cinikin.’ ”

  18. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.

  19. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.

  20. “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango.

  21. Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa.

  22. Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako, amma ka ƙi ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci amma ba ka ce ufam ba.

  23. Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

  24. Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,

  25. Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.”