Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pillars

42 ayoyi · 27 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri.

  2. Kashegari da sassafe, sai Yaƙub ya ɗauki dutsen da ya yi matashin kai da shi, ya kafa shi al’amudi, ya kuma zuba mai a kansa.

  3. Ni ne Allah na Betel, inda ka zuba wa al’amudi mai, da kuma inda ka yi mini alkawari. Yanzu ka bar wannan ƙasa nan take, ka koma ƙasarka ta ainihi.’ ”

  4. Laban ya kuma ce wa Yaƙub, “Ga wannan tsibi, ga kuma wannan al’amudin da na kafa tsakaninka da ni.

  5. Wannan tsibin shi ne shaida, wannan al’amudi kuma shaida ne, cewa ba zan tsallake wannan tsibi zuwa gefenka don in cuce ka ba, kai kuma ba za ka tsallake wannan tsibi da al’amudi zuwa gefena don ka cuce ni ba.

  6. Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.

  7. Da rana Ubangiji yakan ja gabansu a cikin al’amudin girgije domin yă bishe su a kan hanyarsu, da dare kuma a cikin al’amudin wuta domin yă ba su haske, domin su iya tafiya dare da rana.

  8. Al’amudan nan biyu, na girgije da na wuta, ba su daina yi wa jama’a jagora ba.

  9. Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.

  10. Ka rataye shi a bisa dogayen sanduna huɗun nan na itacen ƙirya, waɗanda aka dalaye da zinariya, waɗanda suke tsaya a rammuka huɗu na azurfa.

  11. Ka yi ƙugiyoyin zinariya domin wannan labule da katakai itacen ƙirya biyar, waɗanda aka dalaye da zinariya. Ka kuma yi zubi na tagulla biyar dominsu.

  12. Suka yi dogayen sanduna huɗu na itacen ƙirya dominsa, suka dalaye su da zinariya. Suka yi ƙugiya na zinariya dominsa, suka yi rammuka huɗu da azurfa.

  13. suka kuma yi dogayen sanduna biyar da ƙugiya dominsu. Suka dalaye saman dogayen sandunan da abin daurinsu da zinariya, suka kuma yi rammukansu guda biyar da tagulla.

  14. “ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  15. Sai Ubangiji ya sauko a cikin ginshiƙin girgije; ya tsaya a bakin ƙofar Tenti, ya kira Haruna da Miriyam. Sa’ad da su biyu suka gusa gaba,

  16. Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta.

  17. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.

  18. Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau.

  19. Sai Yoshuwa ya kafa duwatsu goma sha biyun nan da suka ɗauko daga Urdun.

  20. Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.”

  21. Sa’an nan Samson ya kai hannuwansa ga ginshiƙan waɗanda haikalin yake a kai, ya jingina jikinsa, hannunsa dama yana a ɗaya, hannun hagu kuma na ɗayan,

  22. Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.

  23. A lokacin da Absalom yake da rai, Absalom ya gina wa kansa al’amudin tunawa, a Kwarin Sarki, gama ya yi tunani ya ce, “Ba ni da ɗa namiji wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Sai ya kira ginshiƙin da sunansa, ana kuwa kira shi Al’amudin Absalom har wa yau.

  24. Ya yi ginshiƙan tagulla, kowanne tsayinsa kamu goma sha takwas, ya kuma yi guru mai kamu goma sha biyu, kewaye da shi.

  25. Ya yi dajiyoyi biyu na zubin tagulla don yă sa a bisa ginshiƙai; kowace dajiya tsayinta kamu biyar ne.