Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pharaoh

35 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Abram ya isa Masar, Masarawa suka ga cewa Saira kyakkyawa mace ce ƙwarai.

  2. Sa’ad da fadawan Fir’auna suka gan ta kuwa, sai suka yabe ta wajen Fir’auna, aka kuwa kawo ta cikin fadarsa.

  3. Ya mutunta Abram sosai saboda ita, Abram kuwa ya mallaki tumaki da shanu, da jakuna maza da mata, da bayi maza da mata, da kuma raƙuma.

  4. Amma Ubangiji ya wahalar da Fir’auna da gidansa da cututtuka masu zafi saboda Saira, matar Abram.

  5. Saboda haka Fir’auna ya kira Abram ya ce, “Me ke nan ka yi mini? Me ya sa ba ka faɗa mini cewa ita matarka ce ba?

  6. Don me ka ruɗe ni cewa, ‘Ita ’yar’uwata ce,’ har na ɗauke ta tă zama matata? To, ga matarka. Ɗauke ta ka tafi.”

  7. Sa’an nan Fir’auna ya yi wa mutanensa umarni a kan Abram, suka kuwa sallame shi tare da matarsa da kuma dukan abin da yake da shi.

  8. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.

  9. (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga ’yarsa, matar Solomon.

  10. Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima.

  11. Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci.

  12. Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi ’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure.

  13. ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da ’ya’yan Fir’auna.

  14. Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.”

  15. Fir’auna ya tambaye shi, ya ce, “Me ka rasa a nan da kake so ka koma garinka?” Ya ce, “Ba kome, amma ka dai bar ni in tafi!”

  16. Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.

  17. Yayinda Yosiya yake sarki, Fir’auna Neko, sarkin Masar ya haura zuwa Kogin Yuferites don yă taimaki sarkin Assuriya da yaƙi. Sarki Yosiya kuwa ya yi ƙoƙari ya hana shi wucewa, sa’ad da Fir’auna Neko ya gan shi, sai ya kashe shi a filin yaƙi a Megiddo.

  18. Bayin Yosiya suka ɗauko gawarsa daga Megiddo suka kai Urushalima, suka binne shi a kabarinsa. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa.

  19. Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna.

  20. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi.

  21. Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya.

  22. Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.

  23. Yehohiyakim ya riƙa biyan Fir’auna Neko azurfa da zinariyar da ya umarta. Don yă yi haka sai ya riƙa karɓar azurfa da zinariya daga mutanen ƙasar, kowa bisa ga ƙarfinsa.

  24. Sarkin Masar bai sāke fita daga ƙasarsa don yaƙi ba domin sarkin Babilon ya mamaye yankin, daga Rafin Masar har zuwa Kogin Yuferites.

  25. (Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne ’ya’yan Bitiya ’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura.