Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Commandments

394 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.

  2. Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.

  3. Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.

  4. A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

  5. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

  6. amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.

  7. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!

  8. Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,

  9. gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

  10. Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba,

  11. don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya

  12. kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.

  13. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!

  14. Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

  15. Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

  16. A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

  17. Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  18. Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa,

  19. “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”?

  20. Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane.

  21. Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.

  22. Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.

  23. Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.

  24. Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku.

  25. Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa