Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Commandments: General references

83 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. A ranan nan kowa zai faɗa wa ɗanka, ‘Ina yin haka saboda abin da Ubangiji ya yi mini, sa’ad da na fita daga Masar.’

  2. Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko.

  3. Dole ku kiyaye wannan farilla kowace shekara a lokacinta.

  4. “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.

  5. Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba.

  6. Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,

  7. amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

  8. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

  9. Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki.

  10. Kwana shida za ka yi dukan aikinka,

  11. amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.

  12. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  13. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  14. Ba za ka yi kisankai ba.

  15. Ba za ka yi zina ba.

  16. Ba za ka yi sata ba.

  17. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  18. Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

  19. Ku kula, ku kuma lura da kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da idanunku suka gani, ko kuwa ku bari su fita daga zuciyarku muddin ranku. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, da ’ya’yan ’ya’yanku.

  20. Ku tuna da ranar da kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa’ad da ya ce mini, “Ka tara mutane a gabana, don su ji maganata, su koya yin mini bangirma muddin ransu a ƙasar, su kuma iya koyar da su ga ’ya’yansu.”

  21. “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

  22. “Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba.

  23. Ba za ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa ba.

  24. Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni.

  25. Amma nakan nuna ƙauna ga dubban tsararraki na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye dokokina.