Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Astronomy

50 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Dukan haskokin sammai za su zama duhu a kanka; zan kawo duhu a kan ƙasarka, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  2. “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba;

  3. taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’

  4. Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara,

  5. domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu.

  6. Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.

  7. Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.

  8. Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini,

  9. taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi.

  10. Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.

  11. Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa

  12. sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.

  13. Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare.

  14. Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis.

  15. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama.

  16. Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta.

  17. Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa,

  18. Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa.

  19. Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.

  20. Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta.

  21. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.

  22. Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi.

  23. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi.

  24. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne.

  25. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.