Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Astronomy: General references

17 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da General references

  1. “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?

  2. Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje?

  3. Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

  5. Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani.

  6. Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su.

  7. Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,

  8. wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa, kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.

  9. Takan taso daga ƙarshen sammai ta kewaye zuwa wancan; babu abin da yake ɓuya wa zafinta.

  10. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  11. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  12. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  13. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  14. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  15. Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

  16. “In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,” in ji Ubangiji, “to, sai zuriyar Isra’ila ta daina zama al’umma a gabana.”

  17. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In a iya auna sammai a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan saboda dukan abin da suka yi,” in ji Ubangiji.