Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 26:8kusan 610 K.H.

    Amma da Irmiya ya gama faɗar wa dukan mutanen abin da Ubangiji ya umarce shi ya faɗa, sai firistoci, annabawa da dukan mutane suka kama shi suka ce, “Mutuwa za ka yi!

  2. Irmiya 26:9kusan 610 K.H.

    Me ya sa ka yi annabci da sunan Ubangiji cewa wannan gida zai zama kamar Shilo, wannan birni kuma zai zama kango da hamada?” Sai duk mutane suka tattaru kewaye da Irmiya a cikin gidan Ubangiji.

  3. Irmiya 26:10kusan 610 K.H.

    Da fadawan Yahuda suka ji haka, sai suka haura daga fada zuwa gidan Ubangiji suka zazzauna a wuraren zamansu a mashigin Sabuwar Ƙofar gidan Ubangiji.

  4. Irmiya 26:11kusan 610 K.H.

    Sa’an nan firistoci da annabawa suka ce wa fadawan da dukan mutane, “Mutumin nan ya cancanci hukuncin kisa gama ya yi annabci gāba da wannan birni. Ku kun ji da kunnuwanku!”

  5. Irmiya 26:12kusan 610 K.H.

    Sai Irmiya ya ce wa dukan fadawa da kuma dukan mutane, “Ubangiji ya aiko ni in yi annabci gāba da wannan gida da wannan birni dukan abin da na faɗa.

  6. Irmiya 26:13kusan 610 K.H.

    Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.

  7. Irmiya 26:14kusan 610 K.H.

    Game da ni dai, ina a hannuwanku; ku yi duk abin da kuka ga ya yi kyau, ya kuma dace a gare ku.

  8. Irmiya 26:15kusan 610 K.H.

    Ku tabbata dai, cewa in kuka kashe ni, za ku jawo wa kanku alhakin jini marar laifi a kanku da a kan birnin nan da kuma a kan masu zama a cikinsa, gama a gaskiya Ubangiji ne ya aiko ni wurinku domin in faɗa muku dukan maganan nan a kunnuwanku.”

  9. Irmiya 26:16kusan 610 K.H.

    Sai fadawa da dukan mutane suka ce wa firistoci da annabawa. “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”

  10. Irmiya 26:17kusan 610 K.H.

    Waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka zo gaba suka ce wa dukan taron jama’a,

  11. Irmiya 26:18kusan 610 K.H.

    “Mika mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya sarkin Yahuda. Ya ce wa dukan mutanen Yahuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “ ‘Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za tă zama tsibin juji, ƙwanƙolin dutsen haikali kuwa zai zama kurmi.’

  12. Irmiya 26:19kusan 610 K.H.

    “Hezekiya sarkin Yahuda ko kuwa wani a Yahuda ya kashe shi? Ashe, Hezekiya bai ji tsoron Ubangiji ya nemi tagomashinsa ba? Ubangiji kuwa bai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kansu ba? Muna gab da jawo wa kanmu muguwar masifa!”

  13. Irmiya 26:20kusan 610 K.H.

    (To, fa, Uriya ɗan Shemahiya daga Kiriyat Yeyarim wani mutum ne wanda ya yi annabci da sunan Ubangiji; ya yi annabci irin abu ɗaya gāba da wannan birni da wannan ƙasa yadda Irmiya ya yi.

  14. Irmiya 26:21kusan 610 K.H.

    Da sarki Yehohiyakim da dukan fadawansa da ma’aikatansa suka ji wannan magana, sai sarki ya nemi a kashe shi. Amma Uriya ya ji wannan shiri sai ya gudu zuwa Masar don tsoro.

  15. Irmiya 26:22kusan 610 K.H.

    Sarki Yehohiyakim ya aiki Elnatan ɗan Akbor zuwa Masar, tare da waɗansu mutane.

  16. Irmiya 26:23kusan 610 K.H.

    Suka dawo da Uriya daga Masar suka kawo shi wurin Sarki Yehohiyakim, wanda ya kashe shi da takobi aka kuma jefar da gawarsa a makabartar talakawa.)

  17. Irmiya 26:24kusan 610 K.H.

    Bugu da ƙari, Ahikam ɗan Shafan ya goyi bayan Irmiya, saboda haka ba a ba da shi ga mutane don su kashe shi ba.

  18. Irmiya 27:1kusan 595 K.H.

    A farkon sarautar Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo wa Irmiya daga Ubangiji.

  19. Irmiya 27:2kusan 595 K.H.

    Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.

  20. Irmiya 27:3kusan 595 K.H.

    Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  21. Irmiya 27:4kusan 595 K.H.

    Ka ba su saƙo wa iyayengijinsu su ce, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Ku faɗa wa iyayengijinku wannan.

  22. Irmiya 27:5kusan 595 K.H.

    Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.

  23. Irmiya 27:6kusan 595 K.H.

    Yanzu zan ba da dukan ƙasashenku ga bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon; zan sa namun jeji ma su bauta masa.

  24. Irmiya 27:7kusan 595 K.H.

    Dukan al’ummai za su bauta masa da ɗansa da kuma jikansa har sai har lokacin ƙasarsa ya kai; sa’an nan al’ummai masu yawa da kuma manyan sarakuna za su kasance a ƙarƙashinsa.

  25. Irmiya 27:8kusan 595 K.H.

    “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.