circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 24:6kusan 598 K.H.
Idanuna za su kula da su don kyautatawarsu, zan kuma komo da su wannan ƙasa. Zan gina su ba zan rushe su ba; zan dasa su ba kuwa zan tumɓuke su ba.
- Irmiya 24:7kusan 598 K.H.
Zan ba su zuciya don su san ni, cewa ni ne Ubangiji. Za su zama mutanena, zan zama Allahnsu, gama za su komo gare ni da dukan zuciyarsu.
- Irmiya 24:8kusan 598 K.H.
“ ‘Amma kamar ’ya’yan ɓauren nan marasa kyau, waɗanda sun yi muni har ba a iya ci,’ in ji Ubangiji, ‘haka zan yi da Zedekiya sarkin Yahuda, fadawansa da sauran mutanen da suka tsira a Urushalima, ko suna a wannan ƙasa ko suna zama a Masar.
- Irmiya 24:9kusan 598 K.H.
Zan mai da su abin ƙyama da masifa ga dukan mulkokin duniya, abin zargi da abin karin magana, abin ba’a da abin la’ana a duk inda zan kore su zuwa.
- Irmiya 24:10kusan 598 K.H.
Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu sai an hallaka su sarai daga ƙasar da na ba su da kuma kakanninsu.’ ”
- Irmiya 25:1kusan 606 K.H.
Magana ta zo wa Irmiya game da dukan mutanen Yahuda a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wadda ta kasance shekara ta fari ta Nebukadnezzar sarkin Babilon.
- Irmiya 25:2kusan 606 K.H.
Saboda haka Irmiya annabi ya ce wa dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima.
- Irmiya 25:3kusan 606 K.H.
Shekaru ashirin da uku, daga shekara ta goma sha uku ta Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda har zuwa wannan rana, maganar Ubangiji ta zo mini na kuma yi muku magana sau da sau, amma ba ku saurara ba.
- Irmiya 25:4kusan 606 K.H.
Ko da yake Ubangiji ya aika dukan bayinsa annabawa gare ku sau da sau, ba ku saurara ba, ba ku kuma kula ba.
- Irmiya 25:5kusan 606 K.H.
Sun ce, “Ku juye yanzu, kowannenku, daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku, za ku kuwa iya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku da kuma kakanninku har abada abadin.
- Irmiya 25:6kusan 606 K.H.
Kada ku bi waɗansu alloli don ku bauta ku kuma yi musu sujada; kada ku tsokane ni in yi fushi da abin da hannuwanku suka yi. Sa’an nan ba zan kawo muku lahani ba.”
- Irmiya 25:7kusan 606 K.H.
“Amma ba ku saurare ni ba,” in ji Ubangiji, “kun tsokane ni da abin da kuka yi da hannuwanku, kuka kuma kawo lahani wa kanku.”
- Irmiya 25:8kusan 606 K.H.
Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Domin kun ƙi ku saurara ga maganata,
- Irmiya 25:9kusan 606 K.H.
zan kira dukan mutanen arewa da bawana Nebukadnezzar sarkin Babilon,” in ji Ubangiji, “zan kuma kawo su su yi gāba da wannan ƙasa da mazaunanta da kuma gāba da dukan al’ummai da suke kewaye. Zan hallaka su sarai in kuma mai da su abin bantsoro da abin dariya, za su kuma zama kufai har abada.
- Irmiya 25:10kusan 606 K.H.
Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.
- Irmiya 25:11kusan 606 K.H.
Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.
- Irmiya 25:12kusan 606 K.H.
“Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada.
- Irmiya 25:13kusan 606 K.H.
Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abubuwan na yi magana a kanta, dukan abubuwan da aka rubuta a wannan littafi, abubuwan da Irmiya kuma ya yi annabci a kan dukan al’ummai.
- Irmiya 25:14kusan 606 K.H.
Su kansu al’ummai da sarakuna masu yawa za su bautar da su; zan sāka musu bisa ga ayyukansu da aikin hannuwansu.”
- Irmiya 25:15kusan 606 K.H.
Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa mini, “Ka karɓi kwaf ruwan inabin nan na fushina a wurina, ka sa dukan al’umman da na aike ka gare su, su sha.
- Irmiya 25:16kusan 606 K.H.
Sa’ad da suka sha, za su yi ta tangaɗi su kuma yi hauka saboda takobin da zan aika a cikinsu.”
- Irmiya 25:17kusan 606 K.H.
Saboda haka na karɓi kwaf daga hannun Ubangiji na sa dukan al’ummai waɗanda ya aiko ni wurinsu su sha.
- Irmiya 25:18kusan 606 K.H.
Urushalima da garuruwan Yahuda, sarakunan da fadawanta, don su mai da su kufai da kuma abin bantsoro da ba’a da la’ana, yadda suke a yau;
- Irmiya 25:19kusan 606 K.H.
Fir’auna sarkin Masar, ma’aikatansa, fadawansa da dukan mutanensa,
- Irmiya 25:20kusan 606 K.H.
da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);