Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 23:21kusan 605 K.H.

    Ban aiki waɗannan annabawa ba, duk da haka sun tafi da saƙonsu; ban yi musu magana ba, duk da haka sun yi annabci.

  2. Irmiya 23:22kusan 605 K.H.

    Amma da a ce sun tsaya a majalisata, da sun yi shelar maganata ga mutanena sun kuma juyar da su daga mugayen hanyoyinsu da kuma daga mugayen ayyukansu.

  3. Irmiya 23:23kusan 605 K.H.

    “Ni ɗin Allah na kusa ne kawai,” in ji Ubangiji, “ba Allah na nesa ba?

  4. Irmiya 23:24kusan 605 K.H.

    Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji “Ban cika sama da ƙasa ba?” In ji Ubangiji.

  5. Irmiya 23:25kusan 605 K.H.

    “Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’

  6. Irmiya 23:26kusan 605 K.H.

    Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu?

  7. Irmiya 23:27kusan 605 K.H.

    Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada.

  8. Irmiya 23:28kusan 605 K.H.

    Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji.

  9. Irmiya 23:29kusan 605 K.H.

    “Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?

  10. Irmiya 23:30kusan 605 K.H.

    “Saboda haka,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke satar maganganuna daga juna.

  11. Irmiya 23:31kusan 605 K.H.

    I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya furta.’

  12. Irmiya 23:32kusan 605 K.H.

    Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.

  13. Irmiya 23:33kusan 605 K.H.

    “Sa’ad da waɗannan mutane, ko annabi ko firist, ya tambaye ka, ‘Mece ce maganarUbangiji?’ Ka ce musu, ‘Wace magana? Zan yashe ku, in ji Ubangiji.’

  14. Irmiya 23:34kusan 605 K.H.

    In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa.

  15. Irmiya 23:35kusan 605 K.H.

    Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’

  16. Irmiya 23:36kusan 605 K.H.

    Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu.

  17. Irmiya 23:37kusan 605 K.H.

    Ga abin da za ku ci gaba da faɗa wa annabi, ‘Mece ce amsar Ubangiji gare ka?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’

  18. Irmiya 23:38kusan 605 K.H.

    Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’

  19. Irmiya 23:39kusan 605 K.H.

    Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku.

  20. Irmiya 23:40kusan 605 K.H.

    Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.”

  21. Irmiya 24:1kusan 598 K.H.

    Bayan Nebukadnezzar ya kwashi Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da fadawa, da masu sana’a da masu zane zanen Yahuda daga Urushalima zuwa Babilon zaman bauta, Ubangiji ya nuna mini kwanduna biyu na ’ya’yan ɓaure ajiye a gaban haikalin Ubangiji.

  22. Irmiya 24:2kusan 598 K.H.

    Kwando guda yana da ’ya’yan ɓaure masu kyau sosai, kamar waɗanda suka nuna da wuri; ɗayan kwandon kuma yana da ’ya’yan ɓaure marasa kyau, sun yi muni har ba a iya ci.

  23. Irmiya 24:3kusan 598 K.H.

    Sa’an nan Ubangiji ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani, Irmiya?” Na ce, “’Ya’yan ɓaure. Masu kyau ɗin suna da kyau sosai, amma munanan sun yi muni har ba a iya ci.”

  24. Irmiya 24:4kusan 598 K.H.

    Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa,

  25. Irmiya 24:5kusan 598 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar ’ya’yan ɓauren nan masu kyau, haka zan kula da mutanen Yahuda waɗanda aka kwaso waɗanda na fisshe su daga wannan wuri zuwa ƙasar Babiloniyawa