circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 25:21kusan 606 K.H.
Edom, Mowab da Ammon;
- Irmiya 25:22kusan 606 K.H.
dukan sarakunan Taya da Sidon; sarakunan bakin teku a ƙetaren teku;
- Irmiya 25:23kusan 606 K.H.
Dedan, Tema, Buz da dukan waɗanda suke a manisantan wurare;
- Irmiya 25:24kusan 606 K.H.
dukan sarakunan Arabiya da dukan sarakunan baƙin da suke zama a hamada;
- Irmiya 25:25kusan 606 K.H.
dukan sarakunan Zimri, Elam da Mediya;
- Irmiya 25:26kusan 606 K.H.
da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha.
- Irmiya 25:27kusan 606 K.H.
“Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’
- Irmiya 25:28kusan 606 K.H.
Amma in suka ki su karɓi kwaf ɗin daga hannunka su sha, ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa dole ku sha!
- Irmiya 25:29kusan 606 K.H.
Ga shi, na sa masifa tă yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana, kuna gani za ku tafi ba hukunci? Ba za ku tafi ba hukunci ba, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi, in ji Ubangiji Maɗaukaki.’
- Irmiya 25:30kusan 606 K.H.
“Yanzu ka yi annabcin dukan waɗannan maganganu a kansu ka kuma ce musu, “ ‘Ubangiji zai yi ruri daga bisa; zai yi tsawa daga mazauninsa mai tsarki ya kuma yi ruri da ƙarfi a kan ƙasarsa. Zai yi ihu kamar waɗanda suke matsin ’ya’yan inabi, yi ihu a kan dukan waɗanda suke zaune a duniya.
- Irmiya 25:31kusan 606 K.H.
Hayaniya za tă taso har iyakar duniya, gama Ubangiji zai kawo tuhume-tuhume a kan al’ummai; zai kawo shari’a a kan dukan ’yan adam ya kuma kashe mugaye da takobi,’ ” in ji Ubangiji.
- Irmiya 25:32kusan 606 K.H.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.”
- Irmiya 25:33kusan 606 K.H.
A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa.
- Irmiya 25:34kusan 606 K.H.
Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau.
- Irmiya 25:35kusan 606 K.H.
Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba, shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba.
- Irmiya 25:36kusan 606 K.H.
Ji kukan makiyaya, kururuwan shugabannin garke, gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo.
- Irmiya 25:37kusan 606 K.H.
Rafi mai gudu a hankali zai zama kango saboda zafin fushin Ubangiji.
- Irmiya 25:38kusan 606 K.H.
Kamar zaki zai bar wurin ɓuyarsa, ƙasarsu kuma za tă zama kufai saboda takobin masu danniya da kuma saboda zafin fushin Ubangiji.
- Irmiya 26:1kusan 610 K.H.
A farkon sarautar Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, wannan magana ta zo daga wurin Ubangiji,
- Irmiya 26:2kusan 610 K.H.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka tsaya a filin gidan Ubangiji ka kuma yi magana ga dukan mutanen garuruwan Yahuda waɗanda suka zo sujada a gidan Ubangiji. Ka faɗa musu kome da na umarce ka; kada ka bar wata magana.
- Irmiya 26:3kusan 610 K.H.
Wataƙila su saurara kowanne kuma ya juyo daga mugun hanyarsa. Sa’an nan in yi juyayi in kuma janye masifar da nake shirin kawo a kansu saboda muguntar da suka aikata.
- Irmiya 26:4kusan 610 K.H.
Ka faɗa musu, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, in ba ku saurare ni, ku kuma bi dokata, wadda na sa a gabanku ba,
- Irmiya 26:5kusan 610 K.H.
in kuma ba ku saurari maganganun bayina annabawa, waɗanda na aika muku sau da sau ba (ko da yake ba ku saurara ba),
- Irmiya 26:6kusan 610 K.H.
to, sai in mai da gidan nan kamar Shilo, birnin nan kuma abin la’ana a cikin al’umman duniya.’ ”
- Irmiya 26:7kusan 610 K.H.
Firistoci, annabawa da dukan mutane suka ji Irmiya yana waɗannan maganganu a gidan Ubangiji.