Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 27:9kusan 595 K.H.

    Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’

  2. Irmiya 27:10kusan 595 K.H.

    Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.

  3. Irmiya 27:11kusan 595 K.H.

    Amma duk al’ummar da ta rusuna da wuyarta a ƙarƙashin karkiyar sarkin Babilon ta kuma bauta masa, zan bar al’ummar ta zauna a ƙasarta ta noma ta, ta kuma zauna a can, in ji Ubangiji.” ’ ”

  4. Irmiya 27:12kusan 595 K.H.

    Na ba da wannan saƙo guda ga Zedekiya sarkin Yahuda. Na ce, “Ka rusunar da wuyanka a ƙarƙashin sarkin Babilon; ka bauta masa da kuma mutanensa, za ka kuwa rayu.

  5. Irmiya 27:13kusan 595 K.H.

    Me ya sa kai da mutanenka za ku mutu saboda takobi, yunwa da annoba waɗanda Ubangiji ya yi barazana wa duk al’ummar da ba za tă bauta wa sarkin Babilon ba?

  6. Irmiya 27:14kusan 595 K.H.

    Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku.

  7. Irmiya 27:15kusan 595 K.H.

    ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ”

  8. Irmiya 27:16kusan 595 K.H.

    Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.

  9. Irmiya 27:17kusan 595 K.H.

    Kada ku saurare su. Ku bauta wa sarkin Babilon, za ku kuwa rayu. Don me wannan birni zai zama kufai?

  10. Irmiya 27:18kusan 595 K.H.

    In su annabawa ne da gaske suna kuma da maganar Ubangiji, bari su roƙi Ubangiji Maɗaukaki ya sa kada a kwashe kayayyakin da suka ragu a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da kuma cikin Urushalima a kai Babilon.

  11. Irmiya 27:19kusan 595 K.H.

    Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,

  12. Irmiya 27:20kusan 595 K.H.

    waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe sa’ad da ya kame Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon tare da dukan manyan mutanen Yahuda da Urushalima,

  13. Irmiya 27:21kusan 595 K.H.

    I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa game da abubuwan da aka bari a gidan Ubangiji da kuma a cikin fadar sarkin Yahuda da Urushalima,

  14. Irmiya 27:22kusan 595 K.H.

    ‘Za a kwashe su zuwa Babilon a can kuwa za su kasance sai ranar da na neme su,’ in ji Ubangiji. ‘Sa’an nan zan komo da su in maido da su wannan wuri.’ ”

  15. Irmiya 28:1kusan 595 K.H.

    A wata na biyar na wannan shekara, shekara ta huɗu, a farkon sarautar Zedekiya sarkin Yahuda, sai annabi Hananiya ɗan Azzur, wanda ya fito daga Gibeyon, ya zo wurina a gidan Ubangiji a gaban firistoci da kuma dukan mutane,

  16. Irmiya 28:2kusan 595 K.H.

    “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Zan karya karkiyar sarkin Babilon.

  17. Irmiya 28:3kusan 595 K.H.

    Cikin shekaru biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwashe daga wannan wuri ya kai Babilon.

  18. Irmiya 28:4kusan 595 K.H.

    Zan kuma komo da Yekoniya ɗan Yehohiyakim sarkin Yahuda da kuma dukan sauran masu zaman bauta daga Yahuda waɗanda suka tafi Babilon,’ in ji Ubangiji, ‘gama zan karya karkiyar sarkin Babilon.’ ”

  19. Irmiya 28:5kusan 595 K.H.

    Sai annabi Irmiya ya amsa wa annabi Hananiya a gaban firistoci da kuma dukan mutane waɗanda suke tsaye a gidan Ubangiji.

  20. Irmiya 28:6kusan 595 K.H.

    Ya ce, “Amin! Ubangiji yă sa yă zama haka! Ubangiji yă cika maganar da ka yi annabci ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubangiji da kuma dukan masu zaman bauta zuwa wannan wuri daga Babilon.

  21. Irmiya 28:7kusan 595 K.H.

    Duk da haka, ka saurari abin da zan faɗa a kunnenka da kuma a kunnen duka mutane,

  22. Irmiya 28:8kusan 595 K.H.

    Daga farko fari annabawan da suka riga ka da ni sun yi annabcin yaƙi, masifa da annoba a kan ƙasashe masu yawa da kuma manyan mulkoki.

  23. Irmiya 28:9kusan 595 K.H.

    Amma annabin da ya yi annabcin salama shi za a ɗauka a matsayin wanda Ubangiji ya aika in har abin da ya furta ya zama gaskiya.”

  24. Irmiya 28:10kusan 595 K.H.

    Sai annabi Hananiya ya cire karkiya daga wuyar annabi Irmiya ya karya ta,

  25. Irmiya 28:11kusan 595 K.H.

    ya ce a gaban dukan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘A haka zan karya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babilon daga wuyan dukan al’ummai a cikin shekaru biyu.’ ” Da wannan, annabi Irmiya ya yi tafiyarsa.