circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 28:12kusan 595 K.H.
Ba a daɗe ba bayan annabi Hananiya ya karya karkiya daga wuyan annabi Irmiya, sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,
- Irmiya 28:13kusan 595 K.H.
“Je ka faɗa wa Hananiya cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka karya karkiyar katako, amma a wurinsa za ka sami karkiyar ƙarfe.
- Irmiya 28:14kusan 595 K.H.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa zan sa karkiyar ƙarfe a wuyan dukan waɗannan al’ummai don in sa su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon, za su kuwa bauta masa. Zan ma sa shi ya mallaki namun jeji.’ ”
- Irmiya 28:15kusan 595 K.H.
Sa’an nan annabi Irmiya ya ce wa annabi Hananiya, “Ka saurara, Hananiya! Ubangiji bai aike ka ba, duk da haka ka lallashe wannan al’umma su dogara ga ƙarya.
- Irmiya 28:16kusan 595 K.H.
Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ”
- Irmiya 28:17kusan 595 K.H.
A wata na bakwai na wannan shekara, annabi Hananiya ya mutu.
- Irmiya 29:1kusan 599 K.H.
Ga abin da yake cikin wasiƙar annabi Irmiya da ya aika daga Urushalima zuwa ga sauran dattawan da suka ragu a cikin masu zaman bauta da kuma zuwa ga firistoci, annabawa da kuma dukan sauran mutanen da Nebukadnezzar ya kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
- Irmiya 29:2kusan 599 K.H.
(Wannan ya faru bayan Sarki Yekoniya da mahaifiyar sarauniya, shugabannin fada da kuma dukan shugabannin Yahuda da Urushalima, gwanayen sana’a da masu sassaƙa suka tafi zaman bauta daga Urushalima.)
- Irmiya 29:3kusan 599 K.H.
Ya ba da wasiƙar ta hannun Eleyasa ɗan Shafan da Gemariya ɗan Hilkiya, waɗanda Zedekiya sarkin Yahuda ya aika wurin Sarki Nebukadnezzar a Babilon. Wasiƙar ta ce,
- Irmiya 29:4kusan 599 K.H.
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ga dukan waɗanda aka kwashe zuwa zaman bauta daga Urushalima zuwa Babilon.
- Irmiya 29:5kusan 599 K.H.
“Ku gina gidaje ku zauna; ku dasa gonaki ku kuma ci abin da suka haifar.
- Irmiya 29:6kusan 599 K.H.
Ku yi aure ku kuma haifi ’ya’ya maza da mata; ku nemi mata wa ’ya’yanku maza, ku kuma ba da ’ya’yanku mata ga aure, saboda su ma za su haifi ’ya’ya maza da mata. Ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.
- Irmiya 29:7kusan 599 K.H.
Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”
- Irmiya 29:8kusan 599 K.H.
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi.
- Irmiya 29:9kusan 599 K.H.
Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji.
- Irmiya 29:10kusan 599 K.H.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sa’ad da shekaru saba’in suka cika a Babilon, zan zo muku in cika alkawarin alherina don in komo da ku zuwa wannan wuri.
- Irmiya 29:11kusan 599 K.H.
Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba.
- Irmiya 29:12kusan 599 K.H.
Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku.
- Irmiya 29:13kusan 599 K.H.
Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
- Irmiya 29:14kusan 599 K.H.
Za ku same ni,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku daga bauta. Zan tattaro ku daga dukan al’ummai in sa ku inda na kore ku,” in ji Ubangiji, “zan kuma komo da ku zuwa wurin da na kwashe ku zuwa zaman bauta.”
- Irmiya 29:15kusan 599 K.H.
Za ku iya ce, “Ubangiji ya tā da annabawa saboda mu a Babilon.”
- Irmiya 29:16kusan 599 K.H.
Amma ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarki, wanda yake zaune a kursiyin Dawuda da kuma dukan mutanen da suka ragu a wannan birni, ’yan’uwanku waɗanda ba su tafi tare da ku zuwa zaman bauta ba.
- Irmiya 29:17kusan 599 K.H.
I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Zan aika da takobi, yunwa da annoba a kansu zan kuma sa su zama kamar ɓaure marar amfani da suka yi munin da ba a iya ci.
- Irmiya 29:18kusan 599 K.H.
Zan fafare su da takobi, yunwa da annoba zan kuma sa su zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya da kuma abin la’ana da abin bantsoro, abin dariya da abin reni, a cikin dukan al’umman da aka kore su zuwa.
- Irmiya 29:19kusan 599 K.H.
Gama ba su saurari maganata ba,” in ji Ubangiji, “maganar da na aika gare su sau da sau ta bayina annabawa. Ku kuma masu zaman bauta ba ku saurara ba,” in ji Ubangiji.