circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 30:13kusan 606 K.H.
Babu wanda zai yi roƙo saboda damuwarku, ba magani domin mikinku babu warkarwa dominku.
- Irmiya 30:14kusan 606 K.H.
Dukan abokanku sun manta da ku; ba su ƙara kulawa da ku. Na buge ku kamar yadda abokin gāba zai yi na kuma hukunta ku yadda mai mugunta zai yi, domin laifinku da girma yake zunubanku kuma da yawa suke.
- Irmiya 30:15kusan 606 K.H.
Me ya sa kuke kuka a kan mikinku, wahalarku da ba ta da magani? Domin laifinku da girma yake da kuma zunubanku masu yawa na yi muku waɗannan abubuwa.
- Irmiya 30:16kusan 606 K.H.
“ ‘Amma duk wanda ya cinye ku za a cinye shi; dukan abokan gābanku za su tafi zaman bauta. Waɗanda suka washe ku su ma za a washe su; dukan waɗanda suka mai da ku ganima su ma zan mai da su ganima.
- Irmiya 30:17kusan 606 K.H.
Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’
- Irmiya 30:18kusan 606 K.H.
“Ga abin da Ubangiji yana cewa, “ ‘Zan mayar da wadatar tentin Yaƙub in kuma ji tausayin wuraren zamansa; za a sāke gina birnin a kufansa, fadar kuwa za tă tsaya a wurin da ya dace da ita.
- Irmiya 30:19kusan 606 K.H.
Daga gare su waƙoƙi za su fito na godiya da kuma sowa ta farin ciki. Zan riɓaɓɓanya su, ba za su kuwa ragu ba; zan kawo musu ɗaukaka, ba kuwa za a ƙasƙanta su ba.
- Irmiya 30:20kusan 606 K.H.
’Ya’yansu za su kasance kamar a kwanakin dā jama’arsu kuma za su kahu a gabana; zan hukunta duk wanda ya zalunce su.
- Irmiya 30:21kusan 606 K.H.
Shugabansu zai zama ɗaya daga cikinsu; mai mulkinsu zai taso daga cikinsu. Zan kawo shi kusa zai kuma zo kusa da ni, gama wane ne zai miƙa kansa don yă yi kusa da ni?’ In ji Ubangiji.
- Irmiya 30:22kusan 606 K.H.
‘Saboda haka za ku zama mutanena, ni kuwa in zama Allahnku.’ ”
- Irmiya 30:23kusan 606 K.H.
Ga shi, hadarin Ubangiji zai fasu cikin hasala, iskar guguwa mai hurawa a kan kawunan mugaye.
- Irmiya 30:24kusan 606 K.H.
Fushi mai zafi na Ubangiji ba zai kawu ba sai ya cika manufofin zuciyarsa gaba ɗaya. A kwanaki masu zuwa za ku gane wannan.
- Irmiya 31:1kusan 606 K.H.
“A lokacin nan, zan zama Allah na dukan kabilan Isra’ila, za su kuma zama mutanena,” in ji Ubangiji.
- Irmiya 31:2kusan 606 K.H.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Mutanen da suka tsere wa takobi za su sami tagomashi a hamada; zan zo don in ba da hutu ga Isra’ila.”
- Irmiya 31:3kusan 606 K.H.
Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa, “Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna; na janye ku da ƙauna marar iyaka.
- Irmiya 31:4kusan 606 K.H.
Zan sāke gina ki za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila. Za ki kuma ɗauki ganganki ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki.
- Irmiya 31:5kusan 606 K.H.
Za ki sāke dasa gonakin inabi a kan tussan Samariya; manoma za su yi shuka a kansu su kuma ji daɗin amfaninsu.
- Irmiya 31:6kusan 606 K.H.
Za a yi ranar da matsara za su tā da murya a kan tuddan Efraim su ce, ‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona, zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”
- Irmiya 31:7kusan 606 K.H.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku rera don farin ciki wa Yaƙub; ku yi sowa don al’ummai da suke nesa. Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka, raguwar Isra’ila.’
- Irmiya 31:8kusan 606 K.H.
Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa in tattara su daga iyakar duniya. A cikinsu makafi da guragu za su kasance, mata masu ciki da matan da suke naƙuda; jama’a mai yawan gaske za su komo.
- Irmiya 31:9kusan 606 K.H.
Za su zo da kuka; za su yi addu’a yayinda nake komo da su. Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba, domin ni ne mahaifin Isra’ila, Efraim kuma ɗan farina ne.
- Irmiya 31:10kusan 606 K.H.
“Ku ji maganar Ubangiji, ya al’ummai; ku yi shelarta a gaban teku masu nesa cewa, ‘Shi wanda ya watsar da Isra’ila zai tattara su zai kuma lura da garkensa kamar makiyayi.’
- Irmiya 31:11kusan 606 K.H.
Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.
- Irmiya 31:12kusan 606 K.H.
Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba.
- Irmiya 31:13kusan 606 K.H.
’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna, haka ma samari da tsofaffi. Zan mai da makokinsu farin ciki; zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki.