circa 800–400 BC
The Hebrew Prophets
God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Irmiya 7:11kusan 610 K.H.
Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon ’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji.
- Irmiya 7:12kusan 610 K.H.
“ ‘Yanzu ku fita zuwa Shilo inda na fara maishe shi wurin zama don Sunana, ku ga abin da na yi masa saboda muguntar mutanen Isra’ila.
- Irmiya 7:13kusan 610 K.H.
Yayinda kuke yin dukan waɗannan abubuwa, in ji Ubangiji, na yi muku magana sau da sau, amma ba ku ji ba; na kira ku, amma ba ku amsa ba.
- Irmiya 7:14kusan 610 K.H.
Saboda haka, abin da na yi wa Shilo shi ne yanzu zan yi wa gidan da ake kira da Sunana, haikalin da kuka dogara a kai, wurin da na ba ku da kuma kakanninku.
- Irmiya 7:15kusan 610 K.H.
Zan kore ku daga gabana, kamar yadda na yi ga dukan ’yan’uwanku, mutanen Efraim.’
- Irmiya 7:16kusan 610 K.H.
“Saboda haka kada ka yi addu’a don wannan mutane ko ka yi wani kuka ko roƙo dominsu, gama ba zan ji ka ba.
- Irmiya 7:17kusan 610 K.H.
Ba ka gani abin da suke yi a biranen Yahuda da kuma a titunan Urushalima?
- Irmiya 7:18kusan 610 K.H.
Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi.
- Irmiya 7:19kusan 610 K.H.
Amma ni ne suke tsokana? In ji Ubangiji Ashe, ba kansu ne suke cuta, suna kunyata kansu ba?
- Irmiya 7:20kusan 610 K.H.
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba.
- Irmiya 7:21kusan 610 K.H.
“ ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa ci gaba, ku ƙara hadayun ƙonawarku da sauran sadakoki ku kuma yi ta cin naman!
- Irmiya 7:22kusan 610 K.H.
Gama sa’ad da na fitar da kakanninku daga Masar na kuma yi musu magana, ban ba su dokoki kawai game da hadayun ƙonawa da sadakoki ba,
- Irmiya 7:23kusan 610 K.H.
amma na ba su wannan umarni cewa ku yi mini biyayya, zan kuwa zama Allahnku ku kuma ku zama mutanena. Ku yi tafiya cikin dukan hanyoyin da na umarce ku, don ku zauna lafiya.
- Irmiya 7:24kusan 610 K.H.
Amma ba su saurara ba, ba su kuwa kula ba; a maimako, suka bi shawarar kansu da ta taurare muguwar zukatansu. Su ja da baya a maimakon yin gaba.
- Irmiya 7:25kusan 610 K.H.
Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa.
- Irmiya 7:26kusan 610 K.H.
Amma ba su saurare ni ba, ba su kula ba. Sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.’
- Irmiya 7:27kusan 610 K.H.
“Sa’ad da ka faɗa musu wannan duka, ba za su saurare ka ba; sa’ad da ka kira su, ba za su amsa ba.
- Irmiya 7:28kusan 610 K.H.
Saboda haka ka faɗa musu cewa, ‘Wannan ce al’ummar da ba tă yi biyayya ga Ubangiji Allahnta ba, ba kuwa ta karɓi gyara ba. Gaskiya ta ƙare; ta ɓace gaba ɗaya daga leɓunansu.
- Irmiya 7:29kusan 610 K.H.
“ ‘Ku aske gashin kanku ku zubar; ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi ’yan zamanin nan ya kuma rabu da su saboda fushin da suka ba shi.
- Irmiya 7:30kusan 610 K.H.
“ ‘Mutanen Yahuda sun yi mugunta a gabana, in ji Ubangiji. Sun kafa gumakansu masu banƙyama a gidan da ake kira da Sunana suka ƙazantar da shi.
- Irmiya 7:31kusan 610 K.H.
Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa ’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba.
- Irmiya 7:32kusan 610 K.H.
Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri.
- Irmiya 7:33kusan 610 K.H.
Sa’an nan gawawwakin wannan mutane za su zama abinci ga tsuntsayen sama da kuma namun jeji, ba za a kuwa sami wani da zai kore su ba.
- Irmiya 7:34kusan 610 K.H.
Zan kawo ƙarshen muryar murna da farin ciki da muryar amarya da ango a garuruwan Yahuda da kuma a titunan Urushalima, gama ƙasar za tă zama kufai.
- Irmiya 8:1kusan 610 K.H.
“ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura.