Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 5:22kusan 612 K.H.

    Bai kamata ku ji tsorona ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata ku yi rawar jiki a gabana ba? Na sa yashi ya zama iyakar teku, madawwamiyar iyakar da ba zai tsallake ba. Raƙuman ruwa za su iya yin hauka, amma ba za su iya haye ta ba; za su iya yin ruri, amma ba za su iya ƙetare ta ba.

  2. Irmiya 5:23kusan 612 K.H.

    Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne; sun kauce suka kuma rabu da ni.

  3. Irmiya 5:24kusan 612 K.H.

    Ba sa faɗa wa kansu, ‘Bari mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, wanda yake ba mu ruwan sama a kan kari na kaka da na bazara, wanda kullum yake tabbatar mana da girbi.’

  4. Irmiya 5:25kusan 612 K.H.

    Laifofinku sun raba ku da waɗannan abubuwa; zunubanku sun hana ku samun alheri.

  5. Irmiya 5:26kusan 612 K.H.

    “A cikin mutanena an sami mugaye waɗanda suke kwanton ɓauna kamar masu sa tarko wa tsuntsaye kamar waɗanda suke kafa tarko don su kama mutane.

  6. Irmiya 5:27kusan 612 K.H.

    Kamar keji cike da tsuntsaye, gidajensu sun cika da ruɗu; sun yi arziki suka kuma zama masu iko

  7. Irmiya 5:28kusan 612 K.H.

    suka kuma yi ƙiba, suka yi bul-bul. Mugayen ayyukansu ba su da iyaka; ba sa wa marayu shari’ar adalci, ba sa kāre ’yancin matalauta.

  8. Irmiya 5:29kusan 612 K.H.

    Bai kamata in hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’umma kamar wannan ba?

  9. Irmiya 5:30kusan 612 K.H.

    “Abin banmamaki da bantsoro ya faru a ƙasar.

  10. Irmiya 5:31kusan 612 K.H.

    Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe?

  11. Irmiya 6:1kusan 612 K.H.

    “Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa.

  12. Irmiya 6:2kusan 612 K.H.

    Zan hallaka Diyar Sihiyona, kyakkyawa da kuma mai laulayi.

  13. Irmiya 6:3kusan 612 K.H.

    Makiyaya da garkunansu za su taso mata; za su kafa tentunansu kewaye da ita, kowanne yana lura da sashensa.”

  14. Irmiya 6:4kusan 612 K.H.

    “Mu shirya don yaƙi da ita! Ku tashi, bari mu fāɗa mata da tsakar rana! Amma, kaito, rana tana fāɗuwa, inuwar yamma kuwa sai ƙaran tsawo take.

  15. Irmiya 6:5kusan 612 K.H.

    Saboda haka ku tashi, bari mu fāɗa mata da dare mu rurrushe kagaranta!”

  16. Irmiya 6:6kusan 612 K.H.

    Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku sassare itatuwan ku tula ƙasa kewaye da Urushalima. Dole a hukunta wannan birni; saboda ya cika da zalunci.

  17. Irmiya 6:7kusan 612 K.H.

    Kamar yadda rijiya takan ba da ruwarta, haka birnin yake da muguntarsa. Ana jin labarin rikici da hallaka a cikinsa; ciwonsa da mikinsa kullum suna a gabana.

  18. Irmiya 6:8kusan 612 K.H.

    Ki ji gargaɗi, ya Urushalima, ko kuwa in juya daga gare ki in mai da ƙasarki kufai don kada wani ya zauna a cikinta.”

  19. Irmiya 6:9kusan 612 K.H.

    Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Bari su yi kalan raguwar Isra’ila a yi kalan sarai yadda ake yi wa inabi; ka sāke miƙa hannunka a kan rassan, kamar mai tattara inabi.”

  20. Irmiya 6:10kusan 612 K.H.

    Ga wa zan yi magana in kuma gargaɗar? Wa zai saurare ni? Kunnuwansu sun toshe don kada su ji. Maganar Ubangiji ta zama abin zargi a gare su; ba sa jin daɗinta.

  21. Irmiya 6:11kusan 612 K.H.

    Amma ina cike da fushin Ubangiji, kuma ba na iya kannewa. “Ka kwararo shi a kan yara a titi da kuma a kan samarin da suka tattaru; za a kama miji da mata a cikinsa, tsofaffi da suka tsufa tukub.

  22. Irmiya 6:12kusan 612 K.H.

    Za a ba da gidajensu ga waɗansu, tare da gonakinsu da matansu, sa’ad da na miƙa hannuna gāba da waɗanda suke zama a ƙasar,” in ji Ubangiji.

  23. Irmiya 6:13kusan 612 K.H.

    “Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya.

  24. Irmiya 6:14kusan 612 K.H.

    Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya.

  25. Irmiya 6:15kusan 612 K.H.

    Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji.