Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 4:3kusan 612 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana ce wa mutanen Yahuda da kuma na Urushalima. “Ku nome ƙasarku kuma kada ku yi shuka cikin ƙayayyuwa.

  2. Irmiya 4:4kusan 612 K.H.

    Ku yi wa kanku kaciya ga Ubangiji ku yi wa zukatanku kaciya, ku mutanen Yahuda da mutanen Urushalima, in ba haka ba hasalata za tă sauko ta ci kamar wuta saboda muguntar da kuka aikata za tă ci ba wanda zai kashe ta.

  3. Irmiya 4:5kusan 612 K.H.

    “Ku yi shela a Yahuda ku kuma furta a Urushalima ku ce, ‘Ku busa ƙaho a ko’ina a ƙasar!’ Ku tā da murya da ƙarfi ku ce, ‘Ku tattaru! Bari mu gudu zuwa birane masu katanga!’

  4. Irmiya 4:6kusan 612 K.H.

    Ku tā da tuta don zuwa Sihiyona! Ku gudu ku nemi mafaka ba tare da jinkiri ba! Gama ina kawowa masifa daga arewa, mummunan hallaka kuwa.”

  5. Irmiya 4:7kusan 612 K.H.

    Zaki ya fito daga ruƙuƙinsa; mai hallakarwar al’ummai ya kama hanya. Ya bar wurinsa don yă lalace ƙasarku. Garuruwanku za su zama kufai babu mazauna.

  6. Irmiya 4:8kusan 612 K.H.

    Saboda haka ku yafa tufafin makoki, ku yi makoki da kuka, gama fushin Ubangiji bai juye daga gare mu ba.

  7. Irmiya 4:9kusan 612 K.H.

    “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “sarki da shugabanni za su fid da zuciya, firistoci za su razana, annabawa kuma za su yi mamaki.”

  8. Irmiya 4:10kusan 612 K.H.

    Sai na ce, “Kash, Ubangiji Mai Iko Duka, yaya ka ruɗi mutanen nan da kuma Urushalima gaba ɗaya haka ta wurin cewa, ‘Za ku zauna lafiya,’ sa’ad da takobi yana a maƙogwaronmu.”

  9. Irmiya 4:11kusan 612 K.H.

    A lokacin za a faɗa wa mutanen nan da kuma Urushalima cewa, “Iska mai zafi daga tuddan hamada za tă hura zuwa wajen mutanena, amma ba don ta sheƙe ko ta rairaye; ba;

  10. Irmiya 4:12kusan 612 K.H.

    iska mafificin ƙarfi da ta fito daga gare ni. Yanzu na zartar da hukuncina a kansu.”

  11. Irmiya 4:13kusan 612 K.H.

    Duba! Yana zuwa kamar gizagizai, kekunan yaƙinsa suna zuwa kamar guguwa, dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaiton mu! Mun shiga uku!

  12. Irmiya 4:14kusan 612 K.H.

    Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto. Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani?

  13. Irmiya 4:15kusan 612 K.H.

    Murya ta shela daga Dan, tana furtawa masifa daga tuddan Efraim.

  14. Irmiya 4:16kusan 612 K.H.

    “A faɗa wa al’ummai wannan, a furta wannan game Urushalima. ‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa, suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda.

  15. Irmiya 4:17kusan 612 K.H.

    Sun kewaye ta kamar masu gadin fili, domin ta yi mini tawaye,’ ” in ji Ubangiji.

  16. Irmiya 4:18kusan 612 K.H.

    “Halinki da ayyukanki sun kawo wannan a kanki. Hukuncinki ke nan. Yana da ɗaci! Ya soke ki har zuciyarki!”

  17. Irmiya 4:19kusan 612 K.H.

    Azabana, azabana! Ina birgima cikin zafi. Azabana, azabar zuciyata! Zuciyata yana bugu a cikina, Ba zan yi shiru ba. Gama na ji karan ƙaho; na ji kirarin yaƙi.

  18. Irmiya 4:20kusan 612 K.H.

    Masifa kan masifa; dukan ƙasar ta zama kufai. Cikin ɗan lokaci aka rurrushe tentuna nawa, mafakata ba zato.

  19. Irmiya 4:21kusan 612 K.H.

    Har yaushe zan dubi tutar yaƙi in kuma ji karar ƙaho?

  20. Irmiya 4:22kusan 612 K.H.

    “Mutanena wawaye ne; ba su san ni ba. Su ’ya’ya ne marasa azanci; ba su da fahimi. Suna da dabarar aikata mugunta; ba su san yadda za su aikata alheri ba.”

  21. Irmiya 4:23kusan 612 K.H.

    Na dubi duniya, na ga cewa marar siffa ce babu kome; sammai kuma, haskensu ya tafi.

  22. Irmiya 4:24kusan 612 K.H.

    Na dubi duwatsu, sai na ga suna makyarkyata; dukan tuddai kuwa suna lilo.

  23. Irmiya 4:25kusan 612 K.H.

    Na duba, sai na ga ba kowa; kowane tsuntsu a sarari da ya tsere.

  24. Irmiya 4:26kusan 612 K.H.

    Na duba, sai na ga ƙasa mai amfani ta zama hamada; dukan garuruwanta sun zama kufai a gaban Ubangiji, a gaban zafin fushinsa.

  25. Irmiya 4:27kusan 612 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Dukan ƙasar za tă zama kufai, ko da yake ba zan hallaka ta gaba ɗaya ba.