Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 4:28kusan 612 K.H.

    Saboda haka duniya za tă yi kuka sammai a bisa kuma za su yi duhu, domin na yi magana kuma ba zan fasa ba, na yanke shawara ba kuwa zan janye ba.”

  2. Irmiya 4:29kusan 612 K.H.

    Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki.

  3. Irmiya 4:30kusan 612 K.H.

    Me kike yi, ya wadda aka ragargaza? Me ya sa kika sanya mulufi kika sa kayan adon zinariya? Me ya sa kika sa wa idanunki tozali? Kin yi kwalliyarki a banza. Masoyanki sun bar ki; suna neman ranki.

  4. Irmiya 4:31kusan 612 K.H.

    Na ji kuka kamar na mace mai naƙuda, nishi kamar na wadda take haihuwa ɗanta na fari, kukan Diyar Sihiyona tana haki, da ƙyar take numfashi, tana miƙa hannuwanta tana cewa, “Wayyo ni kaina! Na suma; an ba da raina ga masu kisana.”

  5. Irmiya 5:1kusan 612 K.H.

    “Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima, ku dudduba ko’ina ku kuma lura, ku bincika cikin dandalinta. Ko za ku sami mutum guda wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya, sai in gafarta wa wannan birni.

  6. Irmiya 5:2kusan 612 K.H.

    Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ duk da haka suna rantsuwar ƙarya.”

  7. Irmiya 5:3kusan 612 K.H.

    Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba.

  8. Irmiya 5:4kusan 612 K.H.

    Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba.

  9. Irmiya 5:5kusan 612 K.H.

    Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin.

  10. Irmiya 5:6kusan 612 K.H.

    Saboda haka zaki daga kurmi zai fāɗa musu, kyarkeci kuma daga hamada zai cinye su, damisa za tă yi musu ƙawanya kusa da garuruwansu yă yayyage duk wanda ya kuskura ya fita, gama tawayensu da girma yake jan bayansu kuma yana da yawa.

  11. Irmiya 5:7kusan 612 K.H.

    “Me zai sa in gafarta muku? ’Ya’yanku sun yashe ni sun yi rantsuwa da allolin da ba alloli ba ne. Na biya musu dukan bukatunsu, duk da haka suka yi zina suka tattaru a gidajen karuwai.

  12. Irmiya 5:8kusan 612 K.H.

    An ciyar da su sosai, kamar ƙosassun ingarmu, masu jaraba, kowanne yana haniniya, yana neman matar maƙwabcinsa.

  13. Irmiya 5:9kusan 612 K.H.

    Ba zan hukunta su saboda wannan ba?” In ji Ubangiji. “Bai kamata in yi ramuwa a kan irin al’ummar nan ba?

  14. Irmiya 5:10kusan 612 K.H.

    “Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su, amma kada ku hallaka su gaba ɗaya. Ku kakkaɓe rassanta, gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne.

  15. Irmiya 5:11kusan 612 K.H.

    Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji.

  16. Irmiya 5:12kusan 612 K.H.

    Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.

  17. Irmiya 5:13kusan 612 K.H.

    Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”

  18. Irmiya 5:14kusan 612 K.H.

    Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.

  19. Irmiya 5:15kusan 612 K.H.

    Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.

  20. Irmiya 5:16kusan 612 K.H.

    Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne; dukansu jarumawa ne.

  21. Irmiya 5:17kusan 612 K.H.

    Za su cinye amfanin gonakinku da abincinku, za su cinye ’ya’yanku maza da mata; za su cinye garkunan tumakinku da na awakinku, za su cinye ’ya’yan inabinku da na ɓaurenku. Da takobi za su hallaka biranenku masu katanga.

  22. Irmiya 5:18kusan 612 K.H.

    “Amma ko a cikin waɗancan kwanaki,” in ji Ubangiji, “ba zan hallaka ku gaba ɗaya ba.

  23. Irmiya 5:19kusan 612 K.H.

    Sa’ad da kuma mutanen suka yi tambaya, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi dukan wannan gare mu?’ Sai ka amsa musu, ‘Yadda kuka yashe ni kuka kuma bauta wa baƙin alloli a ƙasarku, haka yanzu za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’

  24. Irmiya 5:20kusan 612 K.H.

    “Ka sanar da wannan ga gidan Yaƙub ka yi shelarsa a Yahuda.

  25. Irmiya 5:21kusan 612 K.H.

    Ku ji wannan, ku wawaye marasa azanci, waɗanda suke da idanu amma ba sa gani, waɗanda suke da kunnuwa amma ba sa ji.