Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Irmiya 6:16kusan 612 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba; ku nemi hanyoyin dā, ku tambaya inda hanyar mai kyau take, ku yi tafiya a kanta, za ku kuwa sami hutu wa rayukanku. Amma kun ce, ‘Ba za mu bi ta ba.’

  2. Irmiya 6:17kusan 612 K.H.

    Na naɗa muku masu tsaro a kanku na kuma ce, ‘Ku saurari karan ƙaho!’ Amma kuka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’

  3. Irmiya 6:18kusan 612 K.H.

    Saboda haka ku, ya al’ummai; ku lura Ya shaidu, abin da zai faru da su.

  4. Irmiya 6:19kusan 612 K.H.

    Ki ji, ya duniya. Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane, sakayyar ƙulle-ƙullensu, domin ba su saurari maganata ba suka kuma ƙi dokata.

  5. Irmiya 6:20kusan 612 K.H.

    Babu riba a kawo mini turare daga Sheba ko rake mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba; ba na jin daɗin sadakokinku.”

  6. Irmiya 6:21kusan 612 K.H.

    Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena. Mahaifi da ’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna; maƙwabci da abokansa za su hallaka.”

  7. Irmiya 6:22kusan 612 K.H.

    Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Duba, sojoji suna zuwa daga ƙasar arewa; babbar al’umma ce ta yunƙuro daga iyakokin duniya.

  8. Irmiya 6:23kusan 612 K.H.

    Suna riƙe da baka da māshi; mugaye ne kuma marasa tausayi. Motsinsu kamar ƙugin teku ne yayinda suke hawan dawakansu; suna zuwa a jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi don su fāɗa miki, ya Diyar Sihiyona.”

  9. Irmiya 6:24kusan 612 K.H.

    Mun ji labari a kansu, hannuwanmu kuwa suka yi laƙwas. Azaba ta kama mu, zafi kamar na mace mai naƙuda.

  10. Irmiya 6:25kusan 612 K.H.

    Kada ku fita zuwa gonaki ko ku yi tafiya a hanyoyi, gama abokin gāba yana da takobi, kuma akwai razana ko’ina.

  11. Irmiya 6:26kusan 612 K.H.

    Ya mutanena, ku sanya tufafin makoki ku yi birgima a toka; ku yi kuka mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, gama nan da nan mai hallakarwa zai auko mana.

  12. Irmiya 6:27kusan 612 K.H.

    “Na maishe ka mai jarrabawar ƙarfe mutanena ne kuwa ƙarfen, don ka lura ka kuma gwada hanyoyinsu.

  13. Irmiya 6:28kusan 612 K.H.

    Su duka masu taurinkai ne, ’yan tawaye, suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da ƙarfe; dukansu lalatattu ne.

  14. Irmiya 6:29kusan 612 K.H.

    Mazuga yana zuga da ƙarfi don yă ƙone dalma da wuta, amma tacewa yana tafiya a banza; ba a fitar da mugaye.

  15. Irmiya 6:30kusan 612 K.H.

    Ana ce da su azurfar da aka ƙi, gama Ubangiji ya ƙi su.”

  16. Maganar da ta zo wa Irmiya ke nan daga Ubangiji.

  17. Irmiya 7:2kusan 610 K.H.

    “Ka tsaya a ƙofar gidan Ubangiji, a can kuwa ka yi shelar wannan saƙo. “ ‘Ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuda waɗanda suke shiga ta waɗannan ƙofofi don yin sujada ga Ubangiji.

  18. Irmiya 7:3kusan 610 K.H.

    Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allahna Isra’ila, yana cewa ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, zan kuwa bar ku ku zauna a wannan wuri.

  19. Irmiya 7:4kusan 610 K.H.

    Kada ku dogara ga maganganun nan na ruɗarwa cewa, “Wannan shi ne haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji, haikalin Ubangiji!”

  20. Irmiya 7:5kusan 610 K.H.

    In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku,

  21. Irmiya 7:6kusan 610 K.H.

    in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba,

  22. Irmiya 7:7kusan 610 K.H.

    to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin.

  23. Irmiya 7:8kusan 610 K.H.

    Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.

  24. Irmiya 7:9kusan 610 K.H.

    “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba,

  25. Irmiya 7:10kusan 610 K.H.

    sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?