Tsallake zuwa abun ciki

circa 800–400 BC

The Hebrew Prophets

God speaks through Isaiah, Jeremiah, and the minor prophets—calling Israel to repentance and foretelling the coming Messiah.

3,706 ayoyi · 14 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Ishaya 35:10kusan 713 K.H.

    kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  2. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin Sarki Hezekiya, Sennakerib sarkin Assuriya ya kai wa dukan birane masu kagaran Yahuda yaƙi ya kuma kame su.

  3. Ishaya 36:2kusan 710 K.H.

    Sai sarkin Assuriya ya aiki sarkin yaƙinsa tare da mayaƙa masu yawa daga Lakish zuwa wurin Sarki Hezekiya a Urushalima. Sa’ad da sarkin yaƙi ya tsaya a wuriyar Tafkin Tudu, a hanya zuwa Filin Mai Wanki,

  4. Ishaya 36:3kusan 710 K.H.

    Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka fita zuwa wurinsa.

  5. Ishaya 36:4kusan 710 K.H.

    Sai sarkin yaƙin ya ce musu, “Ku faɗa wa Hezekiya. “ ‘Ga abin da babban sarki, sarkin Assuriya, ya faɗa. A kan me kake dangana wannan ƙarfin halinka?

  6. Ishaya 36:5kusan 710 K.H.

    Ka ce kana da dabara da kuma ƙarfin mayaƙa, amma kana magana banza ce kawai. Ga wa ka dogara, da kake tayar mini?

  7. Ishaya 36:6kusan 710 K.H.

    Yanzu duba, kana dogara ga Masar, wannan ɗan tsinken kyauron dogarawa, wanda zai soki hannun mutum yă kuma ji masa rauni in ya dangana a kansa! Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga duk wanda ya dogara da shi.

  8. Ishaya 36:7kusan 710 K.H.

    Kuma in ka ce mini, “Mun dogara ga Ubangiji Allahnmu ne” ba shi ba ne Hezekiya ya rurrushe masujadan kan tudunsa da bagadansa, yana ce wa Yahuda da Urushalima, “Dole ku yi sujada wa gaban wannan bagade”?

  9. Ishaya 36:8kusan 710 K.H.

    “ ‘Yanzu fa, bari in yi ciniki da maigidana, sarki Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sa mahaya a kansu!

  10. Ishaya 36:9kusan 710 K.H.

    Yaya za ka ƙi hafsan mafi ƙanƙanci na hafsoshin maigidana, ko da yake kana dogara ga Masar don kekunan yaƙi da mahayan dawakai?

  11. Ishaya 36:10kusan 710 K.H.

    Ban da haka kuma, na zo ne in faɗa in kuma hallaka wannan ƙasa ba tare da Ubangiji ba? Ubangiji kansa ya faɗa mini in tasar wa wannan ƙasa in kuma hallaka ta.’ ”

  12. Ishaya 36:11kusan 710 K.H.

    Sai Eliyakim, Shebna da Yowa suka ce wa sarkin yaƙin, “Ka yi haƙuri ka yi wa bayinka magana da Arameyanci, da yake muna jinsa. Kada ka yi mana magana da Yahudanci a kunnen mutanen da suke kan katanga.”

  13. Ishaya 36:12kusan 710 K.H.

    Amma sarkin yaƙin ya amsa ya ce, “Kuna tsammani ga maigidanku da ku ne kawai maigidana ya aiko ni in yi waɗannan maganganu, ba ga mutanen da suke zama a kan katanga ba, waɗanda kamar ku, za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu?”

  14. Ishaya 36:13kusan 710 K.H.

    Sa’an nan sarkin yaƙin ya tsaya ya kuma yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji kalmomin babban sarki, sarkin Assuriya!

  15. Ishaya 36:14kusan 710 K.H.

    Ga abin da sarki ya ce kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku. Ba zai cece ku ba!

  16. Ishaya 36:15kusan 710 K.H.

    Kada ku bar Hezekiya ya rarashe ku ku dogara ga Ubangiji sa’ad da ya ce, ‘Tabbatacce Ubangiji zai cece mu; ba za a ba da wannan birni a hannun sarkin Assuriya ba.’

  17. Ishaya 36:16kusan 710 K.H.

    “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya faɗa. Ku nemi salama da ni ku kuma fito zuwa wurina. Ta haka kowa zai ci daga kuringarsa da kuma itacen ɓaurensa ya kuma sha ruwa daga tankinsa,

  18. Ishaya 36:17kusan 710 K.H.

    sai na zo na kuma kwashe ku zuwa ƙasa kamar taku, ƙasar hatsi da kuma sabon ruwan inabi, ƙasar abinci da gonakin inabi.

  19. Ishaya 36:18kusan 710 K.H.

    “Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’ Allahn wata al’umma ya taɓa ceci ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?

  20. Ishaya 36:19kusan 710 K.H.

    Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim? Sun fanshi Samariya daga hannuna?

  21. Ishaya 36:20kusan 710 K.H.

    Wanne cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa daga gare ni? Yaya kuwa Ubangiji zai iya ceci Urushalima daga hannuna?”

  22. Ishaya 36:21kusan 710 K.H.

    Amma mutanen suka yi shiru ba su kuwa ce kome ba, gama sarki ya yi umarni cewa, “Kada ku amsa masa.”

  23. Ishaya 36:22kusan 710 K.H.

    Sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, Shebna magatakarda, da kuma Yowa ɗan Asaf marubuci suka tafi wurin Hezekiya, da rigunansu a kyakkece, suka kuwa faɗa masa abin da sarkin yaƙin ya yi ta farfaɗa.

  24. Ishaya 37:1kusan 710 K.H.

    Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji.

  25. Ishaya 37:2kusan 710 K.H.

    Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz.