Tsallake zuwa abun ciki

circa 930–586 BC

The Divided Kingdom

The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.

1,722 ayoyi · 3 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Sarakuna 7:20kusan 892 K.H.

    Haka kuwa ya kasance, gama mutane sun tattake shi a hanyar shiga, har ya mutu.

  2. 2 Sarakuna 8:1kusan 891 K.H.

    To, Elisha ya riga ya ce wa matan da ya tā da ɗanta daga matattu, “Ki kwashe iyalinki ku tafi duk inda za ku tafi na ɗan lokaci, domin Ubangiji ya sa a yi yunwa na shekara bakwai a ƙasar.”

  3. 2 Sarakuna 8:2kusan 891 K.H.

    Sai macen ta yi kamar yadda mutumin Allah ya faɗa. Ita da iyalinta suka tafi ƙasar Filistiyawa suka zauna shekara bakwai.

  4. 2 Sarakuna 8:3kusan 885 K.H.

    A ƙarshen shekara bakwai ɗin sai ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, ta kuma tafi wajen sarki ta roƙa a mayar mata da gidanta da filinta.

  5. 2 Sarakuna 8:4kusan 885 K.H.

    Sarki kuwa yana magana da Gehazi bawan mutumin Allah, ya ce masa, “Ba ni labarin dukan abubuwan banmamakin da Elisha ya yi.”

  6. 2 Sarakuna 8:5kusan 885 K.H.

    A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.”

  7. 2 Sarakuna 8:6kusan 885 K.H.

    Sarki ya tambayi macen game da al’amarin, ita kuwa ta faɗa masa. Sa’an nan ya sa wani hafsa yă dubi damuwarta ya kuma ce masa, “Ka mayar mata kome da yake nata, haɗe da dukan kuɗin da aka samo daga filin, daga ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.”

  8. 2 Sarakuna 8:7kusan 885 K.H.

    Sai Elisha ya tafi Damaskus, Ben-Hadad mutumin Aram kuwa yana ciwo. Sa’ad da aka faɗa wa sarki, “Mutumin Allah ya hauro tun daga can zuwa nan,”

  9. 2 Sarakuna 8:8kusan 885 K.H.

    sai ya ce wa Hazayel, “Ɗauki wannan tare da kai ka tafi ka taryi mutumin Allah. Ka nemi nufin Ubangiji ta wurinsa; ka tambaye shi, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ”

  10. 2 Sarakuna 8:9kusan 885 K.H.

    Sai Hazayel ya tafi taryen Elisha, ya ɗauka kyauta na kowane irin kaya masu kyau na Damaskus tare da shi a raƙuma arba’in. Ya shiga ya tsaya a gaban Elisha ya ce, “Ɗanka Ben-Hadad na Aram ya aike ni in tambaye ka, ‘Zan warke daga ciwon nan?’ ”

  11. 2 Sarakuna 8:10kusan 885 K.H.

    Elisha ya amsa ya ce, “Je ka ce masa, ‘Ba shakka za ka warke’; ammaUbangiji ya nuna mini cewa ba shakka zai mutu.”

  12. 2 Sarakuna 8:11kusan 885 K.H.

    Sai ya zuba wa Hazayel ido har sai da Hazayel ya ji kunya. Sa’an nan mutumin Allah ya fara kuka.

  13. 2 Sarakuna 8:12kusan 885 K.H.

    Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”

  14. 2 Sarakuna 8:13kusan 885 K.H.

    Hazayel ya ce, “Yaya bawanka, wanda yake kare kawai, zai iya aikata wannan irin abu?” Elisha ya ce, “Ubangiji ya nuna mini cewa za ka zama sarkin Aram.”

  15. 2 Sarakuna 8:14kusan 885 K.H.

    Sai Hazayel ya rabu da Elisha ya koma wurin maigidansa. Da Ben-Hadad ya yi tambaya, “Me Elisha ya ce maka?” Sai Hazayel ya amsa, “Ya faɗa mini cewa tabbatacce za ka warke.”

  16. 2 Sarakuna 8:15kusan 885 K.H.

    Amma kashegari sai ya ɗauki tsumma mai kauri, ya jiƙa shi, ya rufe fuskar sarki da shi, har sai da sarki ya mutu. Sai Hazayel ya gāje shi a matsayin sarki.

  17. 2 Sarakuna 8:16kusan 892 K.H.

    A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda.

  18. 2 Sarakuna 8:17kusan 892 K.H.

    Yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki na tsawon shekara takwas a Urushalima.

  19. 2 Sarakuna 8:18kusan 892 K.H.

    Ya bi gurbin sarakunan Isra’ila, yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji.

  20. 2 Sarakuna 8:19kusan 892 K.H.

    Duk da haka, saboda bawansa Dawuda, Ubangiji bai ragargaza Yahuda ba. Ya riga ya yi alkawari zai bar wa Dawuda magāji har abada.

  21. 2 Sarakuna 8:20kusan 892 K.H.

    A kwanakin Yoram, Edom ta yi wa Yahuda tawaye, ta naɗa wa kanta sarki.

  22. 2 Sarakuna 8:21kusan 892 K.H.

    Saboda haka Yehoram ya tafi Zayir da dukan kekunan yaƙinsa. Sojojin Edom suka kewaye shi a can, amma da dare sai Yoram ya ɓarke ya gudu, sojojinsa kuma suka watse zuwa gidajensu.

  23. 2 Sarakuna 8:22kusan 892 K.H.

    Har yă zuwa yau, Edom tana yi wa Yahuda tawaye. A lokaci ɗaya ne Libna ma ta yi tawaye.

  24. 2 Sarakuna 8:23kusan 892 K.H.

    Game da waɗansu abubuwan da suka faru a zamanin Yoram, ba suna a rubuce a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda ba?

  25. 2 Sarakuna 8:24kusan 892 K.H.

    Yoram ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda. Sai Ahaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.